Rike Hannu A Sallah Ina Ya Samo Asali?

Wato ba shakka wannan magana ta riqe hannu a sallah lamarine mai tsohon tarihi sama da shekara dubu hudu (4,000) da suka wuce. Ya kasance nau’ine na salon bauta ko girmama wani da ake ganin martabarsa da matsayinsa ga masu bin addinin “Zoroastianism” ko kace “Mazdayasna”, wanda akafi sani da “Majusawa”.
Shi wannan addinin ya kasance daga cikin daɗaddun (ancient) addinai wanda ya bulla a kasar Persia, Iran a yanzu kenan. Suna bautawa Allahn su da suka kirashi da “Ahura Mazda” wanda ke nufin (Ubangiji mai hikima). Suna amfani da wuta (fire) wajan bautawa wannan Allahn nasu, wace suke ganin ita wuta tana musalta hasken Allah ne amma ba wai ainihin wutar suke bautawa. To sun kasance yayin bautarsu sukan riqe hannayensu biyu a kirjinsu domin girmamawa ga abin bautarsu.
——————————————————-
To ya akai kuma wasu daga musulmi suka riqeshi a matsayin wani nau’i a ibada?
To yadda lamarin ya kasance kuwa shine, a zamani Khalifa Umar anyi yakin da aka kirashi da “yakin Qadissyya” wanda ya faru tsakanin musulmi da “Sasanian empire. To a wannan yakin ne aka shiga Persia (Iran), a inda rundunar da Khalifa Umar ya tura sukai nasara a yakin da kama bursunan yaki (prisoners of war) daga masu bin addinin zoroast ko ince masu amfani da wuta wajan bautarsu.
To lokacin da aka kawo su waɗannan ribatattun yaki gaban Khalifa Umar sai yaga sun dora hannayensu akan ƙirjinsu, sai ya tambayesu dalilinsu nayin hakan, sai sukace sun kasance sunayin hakan dan girmamawa a yayin da suke gaban wani mai daraja da ƙima. Saboda haka jin haka sai Khalifa yaji ɗadin haka ya kuma cewa musulmi “Ij’aluha fi Salatikum” ma’ana kusanya hakan a cikin sallarku”. To wannan shine asalin yadda akayi riqe hannu ya shigo cikin sallah a musulunci. Amma annabi (s) bai san dashi ba haka kuma sannan a lokacin Khalifa Abu Bkr shima wani bai aikata haka ba. An fara rike hannu a sallah ne a lokacin Khalifa Umar, hakan shima ya jawo sabani a tsakaninsa da wasu daga sahabban Annabi (s).
Ya ishi mutum tunani akan cewar a dukkan malaman mazhabobin nan gudu 4, Malik, Shafi, Hambal da Abu Hanifa babu wanda ya wajabta riƙe hannu a sallah, kai sai ma dai samun sabani akan haka, domin shi Imam Malik cewa yayi “Makruhi” riƙe hannu a sallah, dan haka shi a wurinsa sallarka tafi cikar kamala idan ka saki hannunka a sallah. Dan haka nema zakaga malaman malikiya basa riƙe hannu a sallah.
Akwai wani littafi mai suna “Fiqhus Sunnah na Sayyed Sabiq mutumin Misra (Egypt), a cikin littafin cewa yayi babu wani hadisi daya inganta akan ma’aiki (s) ya riƙe hannu a sallah.
Dan haka yana da kyau mu kara naziri da bincike domin sanin gaskiya a addini.
© Jaafar A Sarki