January 12, 2023

​Real Madrid ta kai wasan karshe na Super Cup na Spain

 

Real Madrid ta doke Valencia a bugun fanareti a wasan kusa da karshe na cin kofin Zakaran-zakaru na Sifaniya wato Spanish Super Cup, a karawar da aka yi a filin wasa na Sarki Fahd da ke babban birnin Saudi Arabia, Riyadh.

Karim Benzema ne ya fara daga raga da bugun fanareti a lokacin wasan inda zakarun na Turai da kuma La Liga suka kasance a gaba.

Sai dai kuma Samuel Lino ya farke kwallon jim kadan da komawa fili daga hutun rabin lokaci, wasan ya kasance 1-1.

Hakan ne ya sa aka tafi bugun fanareti a karshen wasan inda Madrid ta yi nasara da ci 4-3, inda ta ci dukkanin bugunta, yayin da Eray Comert ya barar da tashi, kuma mai tsaron raga Thibaut Courtois ya tare ta Jose Gaya.

SHARE:
Labarin Wasanni 0 Replies to “​Real Madrid ta kai wasan karshe na Super Cup na Spain”