July 28, 2021

RAYUWAR IYALI A MUSLUNCI

RAYUWAR IYALI A MUSLUNCI

Darasi Na Daya (1)

Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Qai, Tsira da amincin Allah su qara tabbata ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammad (sawa) da Ahlinsa tsarkaka.

Aure a muslunci wani abu ne da muslunci ya ke muhimmantar da shi musamman a darasimmu da zai kunshi rayuwar iyali, za mu ga yadda muslunci yake muhimmantar da al’amarin aure, kamar yadda Allah (swt) ya ba da umarni a cikin suratun-Nur, aya ta talatin da biyu (32), yana ce wa: “ Ku aurar da gwagware a cikinku wadanda basu yi aure ba, sun kasance maza ne ko mata, su ake cewa (Aya ma),  wannan dangane da ‘ya ‘ya ye kenan, maza da yammata da samari da zawarawa duk ayi musu aure.

Haka nan ku aurar da salihai daga bayinku maza da mata, Allah (swt) yace: “Idan talakawa ne zai wadata su daga falalarsa, domin shi mai yalwa ne kuma masani”. Kenan aure yana da wannan kimar da muhimmanci ta yadda Allah (swt) ya yi umarni da ayi, kuma talauci bai kamata ya hana mutum aure ba, har ma yana cewa: “Idan sun kasance talakawa ne yakan azurta su”.

A kwai ma wata riwaya da take cewa: “Ku yi aure sai Allah ya wadata ku”, kenan aure akan kansa alheri ne, kuma shi ne tubali na farko da ake gina rayuwar al’umma. A wata riwayar Manzo (sawa) yana cewa: “ A muslunci ba bu ginin da aka gina shi mafi soyuwa ga Allah fiye da rayuwar aure, kenan aure yana da wannan nau’in na kima da daraja da kamala ta yadda gidan aure gida ne da Allah (swt) yake so, kai shi ne ma mafi soyuwa.

Kuma wannan darasin in sha Allahu zai ci gaba da magana a kan ya ya auren zai zama, musamman ayanda rayuwa take caccanzawa, ta hanyar tsatsube-tsatsube da abubuwan da ake jawo su cikin aure ba gaira ba dalili kuma ba shari’a ce ta zo da su ba, wadanda su ne suka tsauwala kuma suka mayar da auren yake wahala a cikin rayuwar mutane.

Lallai aure abu ne mai sauki a kan-kansa ta yadda Allah (swt) ya sanya shi ya zama wasila ne na arziki, kamar yadda muka gani a suratun-Nur, aya ta talatin da biyu (32), cewa lallai a aurar da gwagware daga cikimmu, wato kada a bar al’umma sa sakai.

Akwai ma wata riwaya da aka samo daga Imam Ali (a.s) yana cewa: “Samun gwagware maza da mata masu yawa, wadanda suka isa aure kuma suke da bukatar auren  ba tare da an yi musu auren ba a cikin al’umma, barazana ne a zamantakewar al’umma”.

Kenan aure wani abu ne da ya ke alkinta rayuwa, har ma ya kasance acikin rayuwar iyayemmu da kakanni idan aka ga mutum yana kokarin ya shiga duniya rayuwarsa ta tarbiyya ta gurbata to abu na farko da akan yi sai ace to ayi masa aure, albarkaci dawainiyar da ya ke dauka na aure za ka samu cewa ya natsu ya samu kamun kai.

Wanda ya zuwa yanzu ana samun akasin haka nan, mafi yawan samarin yanzu wadanda za ka ga sun zama ‘yan daba ko yan sara suka, ba bu wannan mas’uliyyar a kansu, saboda haka aure wani abu ne mai gina rayuwa wanda yake da muhimmanci na cikin al’umma, kuma Allah (swt) ya shar’anta shi kana sunna ce ta annabawa, ta yadda Allah (swt) ya yi magana acikin ayoyi da dama cikin littafinsa mai tsarki cewa: Allah (swt) ya sanya annabawa suna da aure kuma suna da zuri’a.

A suratur-Ra’ad, Allah (swt) ya ne cewa: “Hakika mun aiko annabawa kafin kai, kuma muka sanya wa wadannan annabawan mataye da zuri’a”. Almuhim dai a nan shi ne aure yana da muhimmanci wanda muke fatan al’ummarmu za ta ba wa auren muhimmancin da ya dace. In sha Allahu sati mai zuwa za mu ci gaba.

Wasalillahumma Ala Muhammad Wa’ali Muhammad Wa’ajjil Farajahum.

 

Daga Mimbarin:

Sautush-Shi’a Sheikh Bashir Lawal (H)

SHARE:
Rayuwar Iyali 0 Replies to “RAYUWAR IYALI A MUSLUNCI”