Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

August 7, 2021

RAYUWAR IYALI A MUSLUNCI

Darasi Na Daya (2)

Daga Mimbarin Sautus-Shi’a, Sheikh Bashir Lawal Kano (H)

Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Qai, Tsira da amincin Allah su qara tabbata ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammad (sawa) da Ahlinsa tsarkaka.

Kamar yanda muka yi magana a baya kan muhimmancin aure, da irin yadda shari’ar muslunci take karfafansa, da yadda ya kasance sunnar annabawa (a.s) mun gani a baya, abin da ke da muhimmanci dangane da lamarin aure, kamar yadda muka gani a hadisai da ayoyin alkur’ani mai girma.

To shi auren nan fa daya daga cikin abubuwan da ake la’akari da shi wajan kulla shi, shi ne addini, ta bangarorin guda biyu (wato matar da mijin), saboda wani tubali ne wanda da shi ake gina rayuwar al’umma, abubuwan da ake la’akari da shi wajan mijin da za a aura ko matar da za a aura ba janibi ne na zahiri ko abin duniyar da mutum ya mallaka ba.

Shi ya sa ma a shari’a Manzo (sawa) yake cewa: “Idan wanda kuka amincewa addininsa da dabi’unsa ya zo muku neman aure! to ku aurar da shi, idan baku yi haka ba, to fitina ce za ta yadu a bayan kasa da barna (fasadi) mai girma. Don haka a nan gurin muhimmin abu da ya kamata mutane su yi la’akari da shi wajan janibin neman wanda za su aurar masa da ‘ya ya yensu, shi ne su lura da janibin addini da tarbiyya da abinda mutum yake da shi na halayen kwarai.

Kuma ko hadisin ma ya yi la’akari da janibin halaye sannan ya gabatar da shi kafin addini, halayen kirki halayen kwarai, ta yadda ya bayyana cewa idan mai halayen kwarai ya zo muku baku aurar masa ba, to fitina ce da fasadi (barna) za su yadu a doron kasa, a karshe marasa tarbiyya masu wadata na duniya su kadai za su samu damar yin auren.

Kamar yadda aka karfafa bangaren namijin wanda zai yi auren ya zama mai addini da halayen kwarai, to haka ake la’akari da bangaren matar da za a aura, kuma daya daga cikin abin da na so in yi ishara da shi (nuni) a darasin da ya gabata, shi ne tsarabe-tsaraben da aka shigar da su cikin aure da al’adun da ba bu gaira ba bu dalili, wadanda suke hana auren yin armashi da rashin karko, za ka ga kyalkyale banza ne, kaga an yi abu kamar gaske, misali irin iben santa (event center) da ake kirkira ba gaira ba dalili, da wuce gona da irin wajan bushashar auren ya haifar da cewa ga yammata da samari yawa kuma duka suna bukatar  auren amma dawainiyar da auren yake dauke da shi ya sa hakan yana kange su daga zuwa neman auren saboda wannan dawainiyar.

Haka nan su ma iyaye suna jin dawainiyar duk lokacin da mutum zai aurar da diyarsa, ga irin wahalhalun da suke biyo bayan auren, tun daga abubuwan da Allah (swt) bai kallafawa iyaye ba, amma al’ada ta tilasta wa iyayen, duk wannan abubuwan sun hadu sun cakuda lamarin, sun mai da aure ya zama mai wahala, wanda ita kuma shari’ar muslunci ta saukaka shi, kamar yadda ya zo a hadisai da yawan gaske cewa: auren da ya fi albarka shi ne wanda ba a wahala lokacin kulla shi sannan aka yi shi cikin sauki, ta duka bangarorin biyu, ya zama kowa bai galabaita ba, dangin ango da amarya, ta yadda ba a karya jarin ango ba, to irn wannan nau’in na aure ya fi albarka.

Ita abin da shari’a tafi karfafa wa shi ne “Mahar” (sadaki), a ba wa mataye sadakinsu, kuma wannan sadakin shi ne jigo a aure, kuma shi shari’a ta sani, to amma an dabaibaye aure da wasu abubuwa, sannan mace ce akace abawa sadaki ba ita macen ce za ta ba wa miji sadaki ba, amma yau al’ada ta mayar da aure akasin haka, duk wanda zai aurar da ‘yayansu guda biyu namiji da mace, ya tabbatar da cewa abin da zai kashe wa namijin ba zai wuce kaso daya bisa ukun na macen ba, wato abin da za a kashe wa macen ya ninnnika wanda za a kashe wajan auren namiji, misali idan za ka kashe naira dubu dari biyar wajan aurar da danka namiji, to ita ‘ya mace akalla zai iya kaiwa kusan naira miliyan biyu, abin da za ka kashe.

Kayayyakin daki da sauran dawainiya, sannan shi namijin abin da zai kashe bayan sadaki da dukiyar aure za ka samu kayan lefe ne kawai, kuma kayan lefen ma na sa ne tunda gidansa  za ta tafi da shi, amma a karshe idan abu ya shafi ita matar da duk kayan da za a kai mata gidan abubwan da shari’a ta ce (nafaqat) shi namiji shi zai dauki wannan dawainiya amma a yanzu al’ada ta mayar da shi kan dangin ‘ya mace, su ne za su kawo mata komai a bin za ta yi amfani da shi a gidan miji, har ma yana jiran a kawo masa kayan abinci wanda ake cewa “GARA”.

Wadan nan al’adun suna daya daga cikin abin da suke sa aure yake zama mai wahala, sai ka ga mutum ya tara ‘yayaye mata ga sunan rututu, kuma wasu ma suna da manema amma yadda za a aurar da su ya zama da wuya, sakamako irin wadannan abubuwan da al’ada ta tilasta sai hakan ya haifar masa da tsaiko, idan ba a gyara wannan ba yadda yara suke da saurin girma da yanayin rayuwa to Alla kadai ya san abin da zai faru nan gaba a cikin al’ummar mu.

Ga ‘yammatan nan sun isa auren wasunsu suna da manema, amma za ka samu yanayin al’adar da al’umma suka shigar da shi cikin auren ba tare da shar’a ce ta zo da shi ba, hakan yana sa aure yana wahala yana gagara, ko kuma wani lokacin ma a kare da bashi, a yanzu a cikin garin nan munji wata marainiya a daya daga cikin kafar watsa labarai wacca mahaifinta ya rasu ta hanyar hatsarin mota amma da bashi mahaifiyarta ta saya mata kayan daki, an kai rabin kudin bayan aure ta kasa biyan ragowar rabin kudin, haka wadanda suka ba da bashin suka je dakin amaryar suka kwashe kayan dakin, ta zo gidan rediyon tana kuka tana neman tallafi cewa ita marainiya ce ataimaka mata da kayan daki, al’hali shari’ar musluci sadaki aka ce a ba wa mace, kuma da sadakin ne za a yi wa mace kayan dakin, kamar yadda Imam Ali (a.s) ya yi wa Sayyida Zahra (a.s) sadakin da ya ba ta da shi aka saya mata kayan daki.

Saboda Manzon Allah (sawa) shi ya raini Imam Ali (a.s) kuma zai iya yi masa komai, amma saboda yana son ya tabbatar da hukunci na shari’a cewa al’amarin nafaka (ciyarwa) da abin da ya shafi gida da rayuwar aure da kayan amfanin gida da duk abinda a keyi na rayuwar miji da mata Allah (swt) ya daura wa miji ne, mata kawai aka ba ka, har ma takanci riba cikin sadakin, ada idan aka ba wa mace sadaki, bayan an saya mata kayan daki har akan samu rarar da za a saya mata ‘yan dabbobin da za a dinga yi mata kiwo da ire-iren wadannan, amma mu a yanzu akasi ne, al’ada ta canza lamura, saboda haka mu fatammu auren nan a gyara shi, a ci gaba da kula da janibin shari’a kan lamarin aure, Allah (swt) ya sa mu dace, sai mun hadu a zama na gaba.

Wasalillahumma Ala Muhammad Wa’ali Muhammad Wa’ajjil Farajahum.

SHARE:
Rayuwar Iyali One Reply to “RAYUWAR IYALI A MUSLUNCI”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

One comment on “RAYUWAR IYALI A MUSLUNCI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *