December 28, 2023

RASULUL A’AZAM FOUNDATION (RAAF) SAKON TA’AZIYYAR RASUWAR HONOURABLE GHALI UMAR NA-ABBA

 

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

Inna lilLahi wa’inna ilaihi raji’un! Labari ya iso gare mu na rasuwar Mai girma Alh. Ghali Umar Na-Abba, tsohon kakakin majalisar wakilai ta Nijeriya, wanda ya rasu a safiyar jiya Laraba 27/12/2023.
Babu shakka Najeriya ta yi rashin Mukhlisin Dan Siyasa, Arewa ta yi rashin wani shugaba mai kishin jama’arsa, haka al’ummar Musulmi mun yi rashin nagartaccen wakili a fagen Siyasa da shugabancin kasar nan.

A Lokacin da wannan kungiya take jajantawa daukacin ‘yan Nijeriya da al’ummar Musulmin Arewa, muna rokon mambobin kugiyarmu da su yi wa wannan bawan Allah addu’oin neman rahama da karin daukaka a gurin Allah, don kuwa ya taimaka mana a lokacin rayuwarsa wajen gina wannan Mu’assasa mai albarka.

Allah Ya jikansa da rahama, ya shigar da shi cikin ceton Ahlul-Bait (AS).

Daga;
Sheikh Saleh Sani Zaria
Babban Sakatare

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “RASULUL A’AZAM FOUNDATION (RAAF) SAKON TA’AZIYYAR RASUWAR HONOURABLE GHALI UMAR NA-ABBA”