May 9, 2023

​Rasha Ta Yi Maraba Da Mayar Da Syria Cikin Kungiyar Kasashen Larabawa

 

Rasha ta yi maraba da matakin mayar da Syria cikin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da hukumomin da ke da alaka da ita, lamarin da zai kai ga kawar da yanayi na rashin fahimtar juna a tsakanin wasu kasashen gabas ta tsakiya.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha t ace: “Moscow na maraba da wannan mataki da aka dade ana jira, kuma hakan ya kasance sakamako mai ma’ana da tsari, kasancewa kasar Siriya jigo ce mai muhimmanci a kasashen Larabawa,” a cewar Zakharova a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet na ma’aikatar harkokin wajen Rasha.

Ta yi nuni da cewa, Moscow na ci gaba da hulda da manyan kasashen Larabawa, kuma a kullum tana kiransu da su dawo da hulda da Damascus.

Zakharova ya fito fili ya bayyana fatan kasar Rasha na ganin kasashen Larabawa su kara yawan taimakon da suke bayarwa ga kasar Syria, da kuma bayar da tasu gudummawar wajen shawo kan matsalolin sake gina kasar sakamakon takunkumin zalunci da aka kakaba wa Damascus.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova, ta yi nuni da cewa, sake dawo da kasar Siriya a ayyukan kungiyar kasashen Larabawa, zai taimaka wajen kyautata yanayin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, da kuma shawo kan rikicin kasar ta Syria cikin kankanin lokaci.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Rasha Ta Yi Maraba Da Mayar Da Syria Cikin Kungiyar Kasashen Larabawa”