January 30, 2024

​Rasha Ta Yaba Da Gagarumin Ci Gaban Da Ake Samu Tsakaninta Da Kasashen Afirka

Ta hanyoyi da dama, taron kolin Rasha da Afirka da aka gudanar a watan Yulin shekarar 2023 yana ci gaba da gudana har zuwa yau.

Tun daga wannan taron, shugabannin kasashen Afirka uku – Sudan ta Kudu, Equatorial Guinea da kuma, a wannan makon, Chadi – sun ziyarci Moscow. Wannan ba ya hada da wasu manyan tawagogin Afirka – alal misali, ‘yan kwanaki kadan kafin hakan, wata tawaga daga Nijar, karkashin jagorancin Firayim Minista, ta ziyarci Moscow.

Wadannan ziyarce-ziyarcen na zuwa ne bisa la’akari da karuwar kasuwancin da ke tsakanin Rasha da Afirka, da kuma wasu sauye-sauyen tsarin siyasar Afirka da Moscow.

Ziyarar shugaban kasar Chadi Mahamat Deby na da matukar muhimmanci. Wannan dai na daga cikin ziyarorinsa zuwa kasashen waje bayan daidaita al’amuran siyasa a kasar a watan jiya.

Wannan ita ce ziyarar farko da shugaban kasar Chadi ya kai birnin Moscow tun daga shekarar 1968 (Chad ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960) .

Duk da cewa har ya zuwa wannan lokaci, akwai tuntubar juna tsakanin Rasha da Chadi kan matakan siyasa da na tattalin arziki

©VOH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Rasha Ta Yaba Da Gagarumin Ci Gaban Da Ake Samu Tsakaninta Da Kasashen Afirka”