Rasha : Putin, Ya Yi Ta’aziyar Mutuwar Shugaban Kamfanin Wagner

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya yi ta’aziyya game da mutuwar shugaban kamfanin Wagner, Yevgeny Prigozhin, wanda ya mutu a faduwar jirgin sama tare da wasu mutum tara.
Wannan shi ne bayyanin farko da shugaba Putin, ya yi bayan faduwar jirgin data auku ranar Laraba.
Mista Putin, Ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, kuma ya bayyana Prigozhin a matsayin mutum mai baiwar kasuwanci.
A wani sako da ya gabatar ta kafar talabijin, Putin ya ce masu bincike za su yi nazari a kan abin da ya faru, saidai hakan zai dauki lokaci.
Jirgin saman, wanda ya tashi daga Moscow zuwa birnin St Petersburgh, dauke da fasinjoji guda bakwai da ma’aikatan jirgi uku, ya fadi ne ranar Laraba a yankin Tver na arewacin birnin Moscow.
Yevgeny Prigozhin shi ne shugaban kamfanin sojojin hayar Rasha na Wagner, wanda ya kafa a shekara ta 2014.
©VOH