Rasha : Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliyar Iran Zai Kwantar Da Hankali A Yankin.

Da yake jaddada mahimmancin farfado da tattaunawar nukiliyar, wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, Mikhail Ulyanov, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Hanya mafi kyau na hana tashe-tashen hankula a yankin ita ce kammala tattaunawar nukiliyar Iran’’.
“Ci gaban tattaunawar nukiliyar da JCPOA na iya rage tashin hankali da share fagen tattaunawa mai karfi kan tsaron yankin inji Babban jami’in diflomasiyyar na Rasha ya kara da cewa.
Mista Ulyanov ya zargi kasashen yammacin Turai da alhakin rugujewar tattaunawar, ya ce: “A bayyane yake kasashen yammacin duniya ba su shirya don wannan ba. »
Galibin kasashen da ke halartar tattaunawar suna son a gaggauta kammala shawarwarin, sai dai cimma yarjejeniyar ya dogara ne kan kan siyasar Amurka wacce ba ta nuna azama a tattaunawar.
Kafin hakan dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kuma jaddada cewa, idan bangaren Amurka ya yi aiki da gaskiya, to mai yiyuwa ne a cimma matsaya a Vienna.