Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)
December 16, 2022
Rano Air ya ɗauki ɗaliban da Kwankwaso ya kai karatun tukin jirgin sama aiki Sabon kamfanin jigilar jirgin sama, Rano Air, ya bada aiki ga wasu daga cikin daliban da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai kasar Jordan su ka karanci ilmin tukin jirgin sama. Kamfanin, mallakar Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, shahararren mai kasuwancin mai ɗin nan na A.A Rano ya ɗauki daliban aiki ne su bakwai domin su zamo daga cikin matukan jiragen sa. Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa matasan su bakwai, dukkansu ƴan asalin jihar Kano ne. Matasan su ne kamar haka: Capt. Abubakar bello danfulani Capt. Bashir Danladi garba Capt. Habibu yakubu bechi Capt. Yunus Abba yunus Capt. Abdulmajid said Sanjay Capt. Idiris baba idi Capt. Umar gwarzo
SHARE:
Labaran Duniya
0 Replies to “Rano Air ya ɗauki ɗaliban da Kwankwaso ya kai karatun tukin jirgin sama aiki Sabon kamfanin jigilar jirgin sama, Rano Air, ya bada aiki ga wasu daga cikin daliban da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai kasar Jordan su ka karanci ilmin tukin jirgin sama. Kamfanin, mallakar Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, shahararren mai kasuwancin mai ɗin nan na A.A Rano ya ɗauki daliban aiki ne su bakwai domin su zamo daga cikin matukan jiragen sa. Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa matasan su bakwai, dukkansu ƴan asalin jihar Kano ne. Matasan su ne kamar haka: Capt. Abubakar bello danfulani Capt. Bashir Danladi garba Capt. Habibu yakubu bechi Capt. Yunus Abba yunus Capt. Abdulmajid said Sanjay Capt. Idiris baba idi Capt. Umar gwarzo”