November 15, 2022

Ranar bunkasa masana’antun Afirka

Albarkacin ranar bunkasa masana’antun Afirka, wadda ake bikinta a duk ranar 20 ga watan Nuwamba, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a yi hadin gwiwa wajen gina nahiyar Afirka mai wadata.
Mr. Guterres ya ce “A ranar bunkasa masana’antun Afirka, ya kamata mu yi hadin gwiwa wajen gina nahiyar Afrika mai dorewa, zaman lafiya da wadata ga kowa. Kasashen Afirka na fuskantar manyan kalubale, ciki har da tashe-tashen hankula daga masu dauke da makamai, da karuwar tsadar abinci da makamashi, da hauhawar farashin kayayyaki da basussuka. Kazalika kasashen nahiyar na fama da karancin kudaden kasafi, da mummunan tasirin sauyin yanayi.”
Sai dai duk da haka, Guterres ya ce nahiyar Afirka na cikin sassan duniya dake samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, da damar shiga sahun gaba a fannin sauya akalar amfani da makamashi.
Daga nan sai babban jami’in na MDD, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin sassa masu zaman kansu da manyan hukumomin kasa da kasa domin ingiza hade dukkanin sassa, da karfafa juriya, da dorewar ci gaban masana’antu a Afirka.

©cri(Saminu Alhassan)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ranar bunkasa masana’antun Afirka”