August 19, 2021

Ranar Ashura

Daga Muhammad Awwal Bauchi

Wancan daren ya wuce, dogon tarihi ya tafi tare da shi. Ga ranar goma ga watan Muharram nan ta shigo, ranar jini da jihadi da shahada, ranar haduwa da makoma.

 

A bangare guda kuma ga Umar bin Sa’ad nan na shirya sojojinsa, yana gyara su don yakar dan ‘yar Manzon Allah (s.a.w.a) kuma na biyar daga ma’abuta Kisa’i, wadanda Allah Ya farlanta kauna da binsu a kan wannan al’umma da nassin Alkur’ani mai girma.

 

Imam Husaini ya yi shirin yaki. Sai ya fara da kare hemominsu da suka kunshi iyalai mata; sai ya sa a haka rami a kewaye bayan hemomin, sai kuma aka kunna wuta don a hana harin soji a wajen, don ya hada hankali wajen fuskantar abokan gaba ta fuska daya.

 

Bayan hakan sai Imam Husaini (a.s.) ya mike gaban sojojin abokan gaba (mutane Kufa) yana mai huduba, ya shiga tunatar da su wasikunsu da bai’arsu gare shi, amma ba su amsa masa ba, ba su tasirantu da kiransa ba.

 

Sai ya sake komawa ya tsaya ya fuskanci wannan runduna alhali yana kan dokinsa, ya daga Littafin Allah ya bude shi ya dora a kansa, sannan ya ce: “Ya ku wadannan mutane, a tsakani na da ku akwai Littafin Allah da Sunnar kakana Manzon Allah (s.a.w.a)”. Amma ba wanda ya amsa masa daga cikinsu; sai ma Umar bin Sa’ad da ya aiko da ya hori mai rikon tutarsa da ya gabata, sai ya kunna wutar yaki da hannusa mai sabo, ya harba kibiyar farko zuwa rundunar Husaini (a.s.) sannan ya ce: “Ku yi shaida kan cewa ni ne farkon wanda ya yi harbi.”

 

Sai Imam Husaini (a.s.) ya kalli sojojin da suka daura damara, ya lura da su da kyau, amma bai gushe ba kamar dutsen da ya kafu a kasa, zuciyarsa na tsaye da zikirin Allah, duniyar barna ta kaskanta a idonsa, sojin makiya suka karanta a ganinsa, yawan makiya bai tsorata shi ba; sai takubbansu da masunsu suka shiga nufo shi, shi kuwa ya fuskanci Ubangijinsa alhali yana mai daga hannuwansa na kaskantar da kai da fuskantar Allah, yana cewa:

 

“Ya Allah Kai ne amincina ga kowane bakin ciki, kuma Kai ne fatana a cikin kowane tsanani, kuma Kai ne amincina da tanajina cikin kowane al’amari da ya sauka gare ni. So nawa bakin ciki kan raunana zukata, dabaru su karanta a cikinsa, aboki ya gudu a cikin shi kuma makiyi ya daga kai; amma na mika shi gare Ka na kuma kai kara wajen Ka, ina mai wadatuwa da Kai daga waninKa; sai kuwa Ka yaye shi daga gare ni. Domin Kai ne majibincin kowace ni’ima kuma ma’abucin kowane kyakkyawan abu kuma karshen kowace bukata(2)”.

 

Wannan shi ne farkon tashin hankali da abin takaici, wanda a sakamakon shi dan gidan Annabci kuma Imamin Musulmi Husaini bin Ali bin Abi Dalib, jikan Manzon Allah (s.a.w.a) ya tafi.

 

Kurar yaki ta tashi, bangarorin biyu sun yi fito-na-fito da juna, a dabi’ance sojin Yazidu suna da ikon kashe waccan kungiya mai adadin mutane kadan da ba su wuce mazaje saba’in da takwas ba.

 

Abin takaicin da ya sami Ahlulbaiti (a.s.) da zaluncin da aka yi musu ya siffanta ne a ranar Karbala mai kona rai.

 

Haka matsanancin yaki ya ci gaba, shahidai daga Sahabban Imam Husaini (a.s.) da mutan gidansa suka rika faduwa daya bayan daya, wadannan gwaraza daga iyalan Akil, iyalan Ali da sauran zababbu daga Sahabbansa, kwance yankakku suna warwatse a fagen fama irin watsuwar taurari a sama lokacin bazarar, suna birgima cikin matattarar jini.

 

Hare-hare sun ci gaba a kan wadanda suka saura tare da Husaini (a.s.), suka kewaye su ta sassa da yawa, sai muryar Ibn Sa’ad ke tashi yana kiran sojinsa wadanda suka shiga cikin rundunar Imam Husaini suna kisa suna kwace dukiyoyi, suka kunnawa hemomin wuta, sai mata suka shiga kururuwa yara na ihu da karfi, harshen wuta ya shiga laso hemomin, wadanda ke zaune a cikinsa suka shiga gudu cikin firgita.

 

A wannan hali ne Imam Husaini (a.s.) ya tsaya, a tsakanin shahidan da ke warwatse a fagen fama, ga kururuwan mata da ihun kananan yara na ratsa zuciyarsa, tare da makokin marayu da matan da suka rasa mazansu daga iyalan Muhammadu (s.a.w.a), sai ya tsaya ya yi kira da cewa:

 

“Ko akwai mai kariya ga hurumin Manzon Allah? Ko akwai wani da ya kadaita Allah ya ji tsoron Allah cikin al’amarinmu? Shin ko akwai mai agajin da ke fatan haduwa da Allah a kanmu?”.

 

Ba abin da ya amsa masa sai kururuwar mata da ihun yara. Ba abin da ya saura a gaban Imam Husaini (a.s.) face ya fuskanci mutanen da kansa, ya shiga cikin yaki yana mai bayyana gwarzantakarsa, alhali zuciyarsa na cike da kauna, tausayi da tsoro a kan iyalinsa da iyalin masu taimaka masa da marayun shahidai.

 

Husaini ya tabbata cewa ba zai dawo ba daga wannan harin, sai kauna da tausayin uba suka rufe shi a kan dan jaririnsa Abdullahi da ake shayarwa, sai kaunarsa ta rufe shi a lokacin rabuwa, don haka sai ya tsaya a kofar haima ya kira kanwarsa Zainab, ya bukace ta da ta dauko masa dansa don ya gabatar masa da sumbata ta karshe, ya kuma yi masa kallo na karshe.

 

Zainab dai ta dauko shi, sai Husaini (a.s.) ya daga shi don ya rungume shi ya sumbaci busasshen lebensa, amma sai kibiya daga rundunar makiya ta riga shi, ya yin da ta sami tsakiyar wuyan jaririn(3) har sai da ya raba shi da rayuwa, sai ya shiga magyar-magyar din mutuwa da kafafunsa, yana ta birgima cikin jininsa, da jinin yana rubuta kasidar da tafi bayani a diwanin abin takaici, yana magana da zamunan tarihi masu zuwa da wannan zalunci da tashin hankali, wadanda aka daga hankalin iyalan Annabi da su a ranar Ashura.

Me Husaini zai iya yi? Yaya uban da aka tadawa hankali zai yi a lokacin da jinin dan karamin jaririn shi da ba shi da wani laifi ke gudu a hannunsa? Me Husaini zai aikata alhali yana gaini dan jaririnsa an yanka shi a lokacin yana hannunsa?

 

Sai Imam Husaini (a.s.) ya tsaya kyam, bai raunana ba, bai girgiza ba, maimakon haka ma sai ya shiga hada jinin a tafin hannunsa, ya daga hannu sama yana mai kai kukansa ga Allah, ya watsa jinin sama yana mai ganawa da Allah da cewa: “Abin da ya sauka gare shi ya yi kadan. Lallai Allah na gani (4)

 

Haka jini ya rika zuba a Karbala, abin takaici ya rika taruwa a sararinsa mai bakin ciki, kishirwa da tsoro na fitowa daga mata da kananan yara a gefen Husaini (a.s.). Sai Imam ya hau dokinsa alhali dan’uwansa Abbas na gabatansa, sai ya fuskanci wajen kogin Furat don ya debowa zukata masu zafi da zukatan iyalan Muhammadu da ke kuna ruwa; sai wani gungun sojoji suka kewaye shi, suka yanke shi daga Abbas, gwarzo kuma mai dauke da tuta. Sai Imam Husaini ya zama yana wani gefe alhali Abbas na wani gefe daban.

 

Gwarzo Abul-Fadhal Abbas(5)ya nuna bajintar yaki matuka, yayin da ya kashe sojin makiya ya dandana musu kudarsu. Lokacin da Abul-Fadhal ya nisanta da dan’uwansa Husaini (a.s.), shi ya shiga fagen fama ne, bai gajiya ba har sai da ya fadi kwance cikin jinin Shahada(6), ya kafa tutar Imam Husaini da yake dauke da ita a ranar Ashura a saharar Karbala, ya bar ta tana kadawa har abada ba tare da ranaku sun tsufar da ita ba, kuma masu dagawa ba su iya sauke ta ba.

 

Ta daya bangaren kuma, Imam Husaini (a.s.) ya ratsa fagen fama, yana kokarin isa zuwa kogin Furat, sai wasu gungun sojin ‘yan adawa suka sake sha masa gaba, sai daya daga sojin Ibn Sa’ad ya harbe shi da kibiyar da ta sami jikinsa, sai Imam Husaini (a.s.) ya tsige mashin, ya shiga tara jinin da ke zuba a hannunsa, sannan sai ya jefa jinin sama yana cewa:

 

“Ya Allah ina kai kuka gare Ka kan abin da ake yiwa dan ‘yar AnnabinKa (7).

 

Sai Imam Husaini ya kalli abin da ke kewaye da shi, ya mika ganinsa har zuwa karshen filin, bai ga daya daga Sahabbansa da mutan gidansa ba face yana kwance cikin jinin shahada gabubbansa a daddatse, sai ya shiga fadar kalmomin nan nasa tabbatattu:

 

Zan ci gaba, ai mutuwa ba tsiraici ba ne ga mutum.

 

Idan dai ya nufi gaskiya tare da jihadi yana Musulmi.

 

Ya kuma yi koyi da mutanen kirki da kan shi.

 

Ya kuma kyale mutanen banza ya sabawa masu laifi.

 

In na rayu ba nadama ba in kuma na mutu ba zargi.

 

Ya ishe ka kaskanci ka rayu alhali an dabbe ka.

 

Ga Husaini nan shi kadai, yana rike da takobin Manzon Allah (s.a.w.a), a cikin kirjinsa kuma da zuciyar Ali (a.s.), a hannunsa ga tutar gaskiya, a harshensa da kalmar takawa; ya tsaya a gaban dakarun da suka nutsu cikin laifuka kuma shaidan ya fi karfinsu, ba abin da suke tunani face kashe Husaini da wulakanta gawarsa.

 

To ga shi nan a ranar da aka yi alkawarinta, wadda Manzo (s.a.w.a) ya bayar da labarinta. Ga turbayar da aka masa albishir da ita tuntuni.

 

Husaini (a.s.) ya dauki takobinsa, sai ya shiga daga muryarsa kamar yadda aka saba a yaki da tsare-tsarensa, ya shiga zubar da mayakansu, yana kalubalantarsu da karfin gaske da kwazon da ba shi da kamanni. Abokin hamayya ba ya fito-na-fito da shi har sai ya dukar da shi da takobinsa dukarwa ta kaskanci da faduwa.

 

Zuciyar Imam Husaini (a.s.) ta ta’allaka da hemomin nan da abin da ya saura a cikinsu na mata da kananan yara wadanda suka tsira daga kisa da keta haddi. Sai ya shiga kira, a lokacin da sojojin Umar Ibn Sa’ad suka yi wa Imam Husaini kawanya har suka shiga tsakaninsa da iyalinsa, sai ya yi musu tsawa da cewa:

 

“Ni ke yaki da ku, mata ba ruwan su, ku kyale daga iyalina tun da ga ni a raye a tare da ku(8).

 

Kunnuwa da zukatan wadancan masu kunnen-kashi sun kurumta daga jin zancen dan ‘yar Manzon Allah (s.a.w.a), sai Shimr bin Zil-Jaushan tare da wasu mutanensa su goma, ya nufi wajen hemomin da iyalan Husaini ke ciki; sai Imam ya kara daka musu tsawa da cewa:

 

“Kaiconku! In har ba ku da addini kuma ba ku tsoron ranar kiyama, to ku zama ‘ya’ya mana masu lissafi! Ku kawar da jahilanku da kangararrunku daga iyalina”.

 

Sai Ibn Zil-Jaushin ya ce: “Ka sami haka, dan Fatima.”

 

Matsanantan hare-hare sun ci gaba alhali Husaini (a.s.) na tsakiyar wannan runduna mai tarin mayaka, ya rika tsaga su har lokacin da daya daga sojojin makiya ya yarbo kibiyarsa da ta sauka a wuyan Imam Husaini (a.s.). Daga sai sukan masu da takubba suka ratsa jikin Husaini (a.s.) har sai da raunuka suka kai sittin da bakwai a jikinsa(9).

 

Imam Husaini (a.s.) ya rungumi saharar Daffi (Karbala), jikinsa mai tsarki ya kwanta mike a sararin Karbala, daga hanyoyin jinin wuyansa jini na kwarara; amma duk da haka ruhin kiyayya da dabbanci wanda ya cika zukatan masu laifin nan bai yi sanyi da abin da suka aikata ba, mugun kullinsu bai kau daga iyaka nan ba, har sai da Shimr bin Zil-Jaushin ya dauki takobinsa na laifi da dabbanci, ya nufi inda Husaini (a.s.) yake kwance; don ya datse kansa daga jikinsa mai tsarki, da haka ya yanke wani reshe daga rassan Annabci, ya sa Zahara bakin ciki ta mafi soyuwa daga ‘ya’yanta; wannan kan da ya dade yana sujjada ga Allah Shi kadai, mai dauke da harshen da ya bai taba wasa da zikirin Allah ba, wanda ya sha fadar cewa:

 

“Ba zan ba ku hannuna -na bai’a- irin bayarwar kaskantattu ba, kuma ba zan yi ikirari da ku irin ikirarin bayi ba”.

 

Kan nan da ke dauke da daukaka (Izza) da kin amincewa ya duka ga masu dagawa ko ya kaskanta goshinsa ga azzalumai. Sai -Shimr- ya kama wuyan Husaini (a.s.), ya shiga raba kan daga gangar jikin, da nufin ya dauki kan a matsayin kyauta ga azzaluman Umayyawa, wadanda suka sayar da addininsu da mutuntakarsu da hankulansu.

 

Bayan haka sai Ibn Sa’ad ya zaburi dokinsa don ya taka jikin Husaini (a.s.) da zuciyarsa mai tsarki.

 

Tsarkakan jikkunan shahidan sun saura har na kwanaki uku a kan sararin Karbala kafin wasu mutane daga kabilar Bani Asad, wadanda ke raye a kusa da fagen dagan, su bisne su.

 

Mujiriman ba su wadata da duk wannan ba, sai da suka dauki Iyalan Manzon Allah (s.a.w.a) da suka kunshi mata da kananan yara da abin da ya saura na ayarin, suka mayar da su fursunonin yaki zuwa Kufa daga nan zuwa Sham, suka bi da su tituna da lunguna, kan Imam Husaini (a.s.) da na sauran Sahabbansa ke gaban wannan ayari da ke cikin bakin ciki. Inna lillahi Wa’inna Ilaihir-Raji’un.

 

Amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya Aba Abdullah al-Husain, ranar da aka haife ka, ranar da ka yi shahada cikin jini a Karbala da kuma ranar da za a tashe ka ka na mai kai karan wadanda suka zalunceka, wadanda suka taimaka wajen hakan da ma dukkan wadanda suka share fagen hakan a gaba ga Kakanka (s.a.w.a).

 

 

SHARE:
Makala 0 Replies to “Ranar Ashura”