January 23, 2023

Ranar 1 ga watan Rajab haihuwan Imam Muhammad Bakir a shekara ta 57 bayan hijira.

A cikin watan Rajab shekara ta 57 bayan hijiran Ma’aiki (s.a.w.a) ne gidan sakon Musulunci ya cika da farin ciki mai girman gaske saboda haihuwar Muhammadu bn Ali bn Husain al-Bakir (a.s), wato Imami na 5 daga cikin Imaman gidan Manzon Allah (s.a.w.a).

Imam Bakir (a.s) dai ya rayu sama da shekaru uku tare da kakansa Imam Husaini (a.s), don haka ya ga waki’ar nan ta Karbala mai tada hankali. Bayan nan kuma ya ci gaba da rayuwa karkashin kulawar mahaifinsa Imam al-Sajjad (a.s) duk tsawon lokacin imamancinsa har lokacin da ya yi shahada, a yayin wannan lokaci dai Imam Bakir (a.s) ya sami ilmummuka na Musulunci da kuma gadon Annabawa (a.s) daga mahaifinsa (a.s).

Wannan yanayi dai ya sanya Imam Bakir (a.s) ya kai wani matsayin na ilmi, daukaka, tunani, kwawawan halaye da dai sauransu da za su ba shi damar jagorantar al’umma gaba daya bayan mahaifinsa.

An ruwaoito al-Zubair bn Muslim al-Makki yana cewa: “Wata rana mun kasance a wajen Jabir bn Abdullah al-Ansari, daya daga cikin sahabban Ma’aiki, sai ga Aliyu bn Husain ya iso tare da dansa Muhammadu al-Bakir, a lokacin yana dan karami, sai Aliyu ya ce wa dansa Muhammadu: ‘Sumbanci kan baffanka’.

Sai Muhammadu ya je ya sumbanci kan Jabir.

Sai Jabir, wanda a lokacin ya makance, ya tambaya cewa: ‘Wane ne wannan?’.

Sai Imam Ali bn Husain ya ce: “Ai dana ne Muhammad”.

Nan take sai Jabir ya rungume shi ya ce: ‘Ya Muhammad! Kakanka Manzon Allah (s.a.w.a) yana gaisheka”.

Sai suka ce: ‘A’a ta ya ya Ya Aba Abdallah?’.

Sai ya ce: “Wata rana na kasance a wajen Manzon Allah (s.a.w.a) a lokacin kuwa Husaini yana zaune a kusa da shi yana wasa da shi, sai ya ce min: ‘Ya Jabir! Za a haifa wa dana Husaini da da za a kira da sunan Ali, a ranar tashin kiyama za a yi kira cewa shugaban masu ibada ya tashi, a lokacin Aliyu bn Husain zai mike. Shi ma Aliyu za a haifa masa da mai suna Muhammad. Ya Jabir! Idan ka hadu da shi ka isar da gaisuwata gare shi, ka sani cewar idan har ka ganshi to sauran kwanakin da suka rage maka ba su da yawa”.

Haka kuwa ya faru, don bayan kwanaki uku da wannan ganawa ne Jabir ya rasu(

Saboda irin dimbin ilmin da yake da shi ne ya sa ake masa lakabi da al-Bakir, wato wanda ya kekketa ilmi, wanda yake bayyana dukkan abubuwan da suka shiga wa al’umma duhu da kuma bayyanar da sirrorin da suke cikin ilmi.

Irin matsayin da Imam al-Bakir (a.s) ya kai ne wajen ilmi da tunani da hangen nesa ya sa al’umma suke taruwa a wajensa don amfanuwa da irin wannan matsayi na ilmi da yake da shi. Ga kadan daga cikin abubuwan da gwarzayen Musulunci suka fadi dangane da shi:

1-    Abdullah bn Atah al-Makki yana cewa: “Ban taba ganin malami a kaskance gaban wani malami ba kamar yadda na gansu (malamai) a gaban Muhammadu bn Ali al-Bakir ba

2-    Ibn al-Imad al-Hanbali yana cewa: Abu Ja’afar Muhammadu al-Bakir ya kasance daga cikin malaman Madina, ana ce masa Bakir ne saboda keta ilmi da ya yi, wato ya keta shi ya san asalinsa da kuma shiga cikinsa

3-    Jabir bn Yazid al-Ja’afi ya kasance idan ya ruwaito hadisi daga gare shi ya kan ce: “Wasiyyin wasiyyai kuma magajin ilmin Annabawa Muhammadu bn Ali.

1-    Imam al-Sadik (a.s) yana cewa: “Babana (Imam Bakir) ya kasance mai yawan zikiri, ya kasance mai ambaton Allah a lokacin da muke tafiya, haka nan idan muna cin abinci ya kasance mai ambaton Allah, haka kuma tattaunawa da mutane ba ta hana shi ambaton Allah. Na kasance ina ganin harshensa na haduwa da saman bakinsa yana mai fadin La’ilaha illallah, ya kan tara mu ya umarce mu da ambaton Allah har rana ta fito, ya kan umarce wadanda suka iya karatu daga cikinmu da su ta karatu, wadanda kuma ba su iya ba da su ta yin zikiri.

2-    Haka nan kuma Imam Sadik (a.s) na cewa: Wata rana na je wajen babana a lokacin kuwa yana ba da sadakan dinare dubu takwas ga mabukatan garin Madina, kana kuma ya ‘yantar da wasu bayi da suka kai kimanin goma sha daya

3-    Hasan bn Kathir yana cewa: Wata rana na isar da kuka ta ta wata bukata da kuma jafa’in ‘yan’uwa ga Abu Ja’afar Muhammadu bn Ali (a.s) sai ya ce min: Mummunan dan’uwa, dan’uwan da yake kasancewa tare da kai a lokacin wadata kana kuma ya kaurace maka lokacin rashi”. Daga nan sai ya umarci wani bawansa da ya zo da wata jaka da ke dauke da dirhami 700 ya ce: Ka ciyar da wannan, idan ya kare ka sanar da ni.

4-    Sulaiman bn Karm ya ce: ‘Abu Ja’afar Muhammadu bn Ali ya kasance ya kan saka mana da dirhami 500 zuwa 600 zuwa 1000, kuma ba ya nuna goyon baya ga ‘yan’uwansa ko na kusa da shi (akan saura)

Imam Bakir (a.s) dai ya kasance yana daukan wadannan nauyi ne ba wai don yana da kudin da ya tara ba ne, face dai shi ya kasance ne kamar yadda dansa Imam Sadik (a.s) ya siffanta shi da cewa: Babana ya kasance mafi karancin kudi daga Ahlulbaitinsa, amma kuma wanda ya fi su nauyi mai yawa.

Www.ahlulbaiti.com

 

 

 

SHARE:
Makala 0 Replies to “Ranar 1 ga watan Rajab haihuwan Imam Muhammad Bakir a shekara ta 57 bayan hijira.”