Ra’isy: Iran Za Ta Cigaba Da Fadada Alakarta Da Kasashen Afirka

Shugaban kasar ta Iran wanda ya karbi takardun kama aiki na sabon jakadan kasar Mali a Iran, ya ce, tun bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran, kasar ta mayar da hankali wajen bunkasa alaka da kasashen nahiyar Afirka.
Shugaban na kasar Iranya kuma ce kasarsa a shirye take ta yi aiki tare da kasashen nahiyar Afirka din ta fuskar tattalin arxiki daga cikinsu har da kasar da Mali
A jiya Lahadi ne dai shugaban kasar ta Iran ya karbi takardun kama aiki na sabon jakadan Mali a Iran, Muhammad Maiga.
Shugaba Ra’isy ya kuma yi ishara da yadda kasashen turai suke wawason arzikin nahiyar Afirka yana mai cewa: kasashen na turai ba sun shiga Afirka ne da niyyar kai taimako ba, sun je ne saboda shimfida mulkin mallaka da kuma wawason arlbarkatun wannan nahiyar.
A nashi gefen,sabon jakadan Mali a Iran din ya jinjinawa jamhuriyar musulunci ta Iran akan cigaban da ta samu, yana mai cewa; masana a nahiyar Afirka suna daukar Iran a matsayin wata kasa wacce take tasowa da karfi ta fuskar tattalin arziki. Don haka suke son kulla alaka da ita, ta wannan fuska.