May 3, 2023

Ra’isi Ya Ce: Duk Wani Kuskuren Da HKI Zata Yi Na Farwa Iran Ta Yaki To Kuwa Shi Ne Na Karshe

 

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa idan haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi kuskuran farwa kasar Iran ta yaki a karon farko, to kuma shi ne na karshe, don masda martanin da Jumhuriyar musulunci ta Iran zata yi, zai kauda haramtacciyar kasar daga samuwa ne.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Talata. A hirar da ta hada shin a tashar talabijin ta Al-mayadeen na kasar Lebanon, ya kuma kara da cewa karfin sojen JMI ba a boye yaki ga kasashen yankin ba. Shugaban ya ce HKI ba zata wanzu bayan duk wani yaki da zai hadata da jumhuriyar muslunci ba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ra’isi Ya Ce: Duk Wani Kuskuren Da HKI Zata Yi Na Farwa Iran Ta Yaki To Kuwa Shi Ne Na Karshe”