May 7, 2023

​Ra’isi: Iran Da Saudiyya Ba Makiyan Juna Ba Ne

 

Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa, kasashen Iran da Saudiyya ba makiyan juna ba ne.

Ibrahim Ra’isi ya bayyana hakan ne a wata zantawa da tashar talabijin din kasar Syria ta gudanar tare da shi, inda aka watsa tattaunawara daren jiya Asabar.

Ya ce ba mu yarda da duk wani furuci ko kalami da ke nuna Saudiyya da Iran a matsayin makiyan juna ba, domin kuwa dukkanin kasashen biyu suna alaka ta addini da tarihi da kuma makwabtaka.

Ya ce jagoran juyin juya halin musunci na Iran ya sha nanata cewa, makiyan Iran da ma al’ummar yankin su ne Amurka da Isra’ila, amma al’ummar musulmi da sauran al’ummomi da ke yankin ba makiyan juna ba ne, kuma sake farfado da alaka tsakanin Iran da Saudiyya ya kara tabbatar da hakan.

Ibahim Ra’si ya kirayi dukkanin al’ummomin yanki das u kara hada karfi da karfe domin yin aiki kafada da kafada da junansu, domin ci gaban al’ummar musulmi da kuma al’ummomin yankin gabas ta tsakiya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Ra’isi: Iran Da Saudiyya Ba Makiyan Juna Ba Ne”