December 30, 2022

Rahotanni daga Brazil na cewa, tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar Pele ya Rasu.

Rahotanni daga Brazil na cewa, tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar Pele, wanda ya taba lashe kofin kwallon kafan duniya har sau uku, ya rasu jiya Alhamis yana da shekaru 82 a duniya, a wani asibiti dake birnin Sao Paulo, bayan ya yi fama da sankarar hanji, kamar yadda likitocinsa suka bayyana a hukumance.
An kwantar da dan kwallon da ake ganin babu kamarsa a fagen tamola a duniya ne, tun ranar 29 ga watan Nuwamba a asibitin Albert Einstein, dake Sao Paulo, sakamakon kamuwa da cutar numfashi bayan ya kamu da cutar COVID-19, da kuma sankarar kaba gami da sankarar hanji.
Da yammacin jiyan ne kuma, asibitin ya sanar da mutuwar “fitaccen dan kwallon”. Rahoton asibitin Albert Einstein na Isra’ila ya bayyana cewa, “Asibitin yana bakin cikin sanar da mutuwar “Edson Arantes do Nascimento, da aka fi sani da Pele, ranar 29 ga watan Disamban shekarar 2022, da karfe 3 da mituna 27 na rana agogon wurin, sakamakon daina aikin da wasu sassan jikinsa suka yi, bayan fama da sankarar hanji dake da alaka da yanayin lafiyar sa na baya.”

©Cri (Ibrahim)

SHARE:
Labarin Wasanni 0 Replies to “Rahotanni daga Brazil na cewa, tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar Pele ya Rasu.”