May 7, 2023

RaayiRiga:Yaushe ne za a ga bayan hare-haren bindiga a Amurka?

#RaayiRiga Yaushe ne za a ga bayan hare-haren bindiga a Amurka?
Daga Lubabatu Lei
“Duk lokacin da na ga an sa hannu cikin jaka, na kan ji tsoro”, furuci ke nan na Osadolor Hernandez, wata daliba a jami’ar Chicago ta kasar Amurka, wadda ta ce, “Har ma ina tunanin ko zan haihu lokacin da na girma, sabo da ba na son ganin yara na suna fuskantar barazanar hare-haren bindiga da ka iya afka musu ba zata, abin da ke sa ni jin tsoro a rayuwata ta kowace rana.” Kalaman nata a hakika ya bayyana yanayin da Amurkawa da yawa ke ciki a halin yanzu.

A jiya ma an kai harin bindiga a wata cibiyar kasuwanci da ke bayan birnin Dallas na jihar Texas ta kasar Amurka, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9, ciki har da yara. A wannan rana kuma, an ji harbin bindiga a unguwar Tacony ta birnin Philadelphia, lamarin da ya hallaka mutane biyu tare da jikkata wani.

In an duba, kusan kowace rana irin wadannan hare-haren bindiga na faruwa a Amurka. A baya baya nan, a ranar 5 ga wata, wani dan bindiga ya harbe wata mace har lahira, tare da ji wa wani rauni a wani filin ajiye motoci da ke Annapolis na jihar Maryland ta kasar Amurka, kafin daga bisani dan bindigar ya kashe kansa. Sai kuma a ranar 4 ga wata, wasu mutane 4 sun halaka sakamakon harin bindiga da ya faru a kauyen Moultrie da ke kudancin jihar Georgia. A ranar 3 ga wata kuma, an kai harin bindiga ga wani asibitin da ke birnin Atlanta, lamarin da ya halaka wata ma’aikaciyar lafiya, tare da jikkata wasu mutane 4……

Gwamnatin Amurka ta sha suka daga gida da ma waje sakamakon matsalar hare haren bindiga da ke ci wa kasar tuwo a kwarya. Sakamakon matsin da gwamnati take fuskanta, a watan Yunin bara, Shugaban kasar Joe Biden ya sa hannu a kan wani shirin doka na kayyade bindigogi, sai dai abin takaici, yau kusan shekara guda ke nan, amma ko kadan ba a ga alamar kyautatuwar yanayin da ake ciki ba. Alkaluman da shafin yanar gizo dake bayani game da matsalar harbin bindiga mai suna “Gun Violence Archive” ya fitar sun shaida cewa, a farkon watannin hudu na bana, mutane kusan dubu 14 sun mutu sakamakon hare-haren bindiga a Amurka, adadin da ya kai kimanin 115 a kowace rana ke nan. Sabo da rashin niyyar daidaita ainihin abubuwan da ke haifar da matsalar bindiga, ya sa shirin dokar ya kasa warware matsalar da ake fuskanta.

Tsohon shugaban kasar Amurka Franklin Roosevelt ya taba bayyana cewa, daya daga cikin ‘yancin dan Adam shi ne “’yanci na rashin jin tsoro”. To, amma kasar da ko rayukan jama’arta ta kasa karewa, ina ake zancenta game da ‘yanci da ma hakkin dan Adam?

Domin moriyar wasu gungun mutane, al’ummar Amurka na fama da munanan hasarorin rayuka. Ko yaushe ne za a ga bayan hare-haren bindiga a Amurka?

 

(Mai Zane:Mustapha Bulama)

SHARE:
Tsokaci 0 Replies to “RaayiRiga:Yaushe ne za a ga bayan hare-haren bindiga a Amurka?”