January 9, 2023

RAAF TA YI ALLAH WADAI GA MUJALLAR CHARLIE HEBDO TA KASAR FARANSA

RAAF TA YI ALLAH WADAI GA MUJALLAR CHARLIE HEBDO TA KASAR FARANSA

Mu’assasa Rasulul A’azam Faundation (RAAF) ta yi Allah wadai da kakkausar murya da nuna bakin cikin ta game da zanen batanci da mujjallar “Charlie Hebdo” ta kasar Faransa ta yi ga Jagoran musulmi kuma jagoran juyin juya hali na Jamhuriyar musulunci ta kasar Iran As-Sayyid Aliyu Husain Al-Khamine’i (D.Z) a ranar Laraba 4/1/2023.

Wannan abinda suka aikata kokari ne na huce haushin kasashen yammacin duniya game kunyar da suka ji sakamakon rashin nasarar da suka yi a baya-bayan nan a kokarin su na ganin bayan wannan gwamnatin ta islama, wacce a duniya ita ce daya tilo da take bayyana izzar musulunci da adalcinsa.

Muna rokon Allah madaukaki da ya cigaba da dafa wa Jamhuriyar islama ta Iran, kuma Ya cigaba da dankwafar da abokan gabarta da ruguza makircin su.

Sanarwa daga Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar
Murtala Isah Dass
9-1-2023

SHARE:
Tsokaci 0 Replies to “RAAF TA YI ALLAH WADAI GA MUJALLAR CHARLIE HEBDO TA KASAR FARANSA”