October 23, 2021

Putin Ya Yaba Da Rawar Da Hezbollah Ke Takawa A Siyasar Lebanon

Daga shafin Hausatv


Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yaba da rawar da kungiyar Hezbollah ke takawa a siyasar kasar Lebanon.

Mista Putin, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a karshen taron tattaunawa ta club din Valdai da aka gudanar a birnin shakatawa na Sochi.

Putin ya kuma ce “Rasha tana tattaunawa da dukkan bangarorin siyasa a Lebanon kuma za ta ci gaba da yin hakan.”

A daye bangaren ya ce Rasha, n afatan samun matsaya guda don cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin Lebanon ba tare da zubar da jinni ba.”

Kalaman nasa na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan kashe mutum 7 tare da jikkata wasu 60 yayin zanga-zangar lumana a Beirut.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Putin Ya Yaba Da Rawar Da Hezbollah Ke Takawa A Siyasar Lebanon”