Putin Ya Ce Yaki Kan Kasar Ukraine Yana Gudana Da Kyau

Shugaban kasar Rasha ya bayyana cewa: Farmakin sojin kasarsa yana gudana yadda aka tsara kan kasar Ukraine
A wata hira da ya yi da kafar yada labaran kasar Rasha a jiya Lahadi shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ya yi furuci da cewa: Farmakin da sojojin Rasha suke ci gaba da kaddamarwa kan kasar Ukraine yana gudana yadda ya kamata, kuma daidai da yadda ma’aikatar tsaro da kuma babban hafsan sojin kasar suka tsara, kamar yadda yake fatan za su kara samun nasarori bayan jihar Solidar.
A nata bangaren, ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da kashe sojojin Ukraine kusan 200 a hare-haren da sojojin Rasha suka kai a ranar Juma’a, kuma ta ce dakarunta na ci gaba da kai hare-hare, wanda ta bayyana a matsayin nasara a yankin Donetsk.
©Hausatv