March 27, 2023

PDP ta dakatar da shugaban jam’iya na Kasa, Dr. Ayu

 

Babbar jam’iyar adawa ta kasa, PDP a jiya lahadi ta sanar da dakatar da shugaban jam’iyar ta Kasa Dakta Iyorchia Ayu bisa zargin hadin kai da jam’iyar adawa.

 

An dakatar da Dr. Ayu ne dai a jiya Lahadi inda wasu zababbun shugabannin jam’iya na yankin Igyorov dake karamar hukumar Gboko ta jihar Benuwai suka dakatar sa shi.

Sakataren jam’iya na yanki ne ya sanar da haka a madadin shugaban jami’ya na yaki Kashi Philip.

A wata takarda da sakataren ya fitar wacce ta samu sanyawar hannun zababbun shugabannin yanki mutum 12 cikin 17. Sakataren ya bayyana cewa sun dakatar da Dr. Ayu ne biyo bayan binciken su da kuma gane cewar ya yi wasu abubuwan da basu dace ba wannan zaben da ta gabata.

Sakataren shi ne da kansa ya karanto takardar dakatar da Dr. Ayu a taron manema labarai. Inda ya bayyana cewa suna takaicin gano gaskiyar cewa Dr. Ayu na wasu abubuwan da kw hana ci gaban jam’iya. Kana a bangare guda an gano cewa bai kada kuri’ar sa ba a zaben gwamnoni da ta gabata. Kana kuma an gano cewa abokan huldar sa mafiya kusanci da shi suna aiki ne ga jam’iyar adawa.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “PDP ta dakatar da shugaban jam’iya na Kasa, Dr. Ayu”