May 10, 2023

Palasdinawa Sun Fara Mayar Da Martani Akan HKI Da Harba Makamai Masu Linzami Akan Tel Aviv

Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ce, a cikin sa’a daya daga fara mayar da martanin ‘yan gwgawarmaya sun harba fiye da makamai masu linzami 100.

Daga cikin inda ‘yan gwagwarmayar su ka harba makamai masu linzami da akwai birnin Tel Aviv, da hakan ya kawo tsaiko a zirga-zirgar jiragen sama a filin jiragen sama na Ben Gorion.

Ya zuwa yanzu ‘yan gwgawarmayar sun ce; makamai masu linzami 300 da su ka harba, akan yankuna mabanbanta na Palasdinu dake karkashin mamaya, somin tabi ne akan abinda zai biyo baya.

Wannan mayar da martanin dai yana zuwa ne a lokacin da HKI take cigaba da kai wa Palasdinawa hare-hare tare da yi musu kisan gilla. A garin Rafah, Palasdinawa biyu ne su ka yi shahada, yayin da wasu takwas su ka jikkata.Adadin shahidan Palasdinawa daga shekaran jiya zuwa yau sun kai 20.

Tuni dai ‘yan sahayoniya su ka fara gudu daga yankunan da suke kusa da zirin Gaza zuwa wuraren masu nisa saboda tsoron abinda zai biyo baya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Palasdinawa Sun Fara Mayar Da Martani Akan HKI Da Harba Makamai Masu Linzami Akan Tel Aviv”