October 10, 2021

Oyo: Mutane da dama sun rasa rayukansu a hatsarin mota

Daga Balarabe Idriss


Rahotanni daga garin Ibadan ya bayyana cewa mutane da dama sun rasa rayukan su inda wasu kuma suka jikkata sakamakon karon motoci guda biyu a kan babban titin Moniya-Iseyin da ke garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Rahoton ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon tukin ganganci da kuma gudu ba bisa ka’ida ba bayan cin kasuwan Kraal na Iseyin.

Wasu shaidun gani-da-ido sun bayyana ma wakilinmu cewa mamatan an dauke su a tare da wadanda suka jikkata zuwa wata asibitin kudi na Iseyin.

wamanda na hukumar kula da ababen hawa da hadarurruka a jahar Oyo, Uche Chukwurah ta tabbatar da faruwar hadarin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Oyo: Mutane da dama sun rasa rayukansu a hatsarin mota”