September 30, 2021

Osun: ‘Yan Sanda Biyu Sun Rasa Rayukan Su Yayin Fashin Bankin WEMA

‘Yan Sanda Biyu Sun Rasa Rayukan Su Yayin Fashin Banki A Osun
Bayan shigar yan fashi Bankin Wema reshen Iragbiji da ke karamar hukumar Boripe na jahar Osun, yan sanda sun bayyana cewa biyu daga cikin jami’an su sun rasa rayukan su a yayin fashin.

Yan fashin da adadin su bai gaza 20 ba sun farmaki bankin Wema da ke reshen Iragbiji da kuma ofishin yan sanda na cikin gari kana kuma suka yi awun gaba da kayan da suka sace.

A wani bayani da mai magana da yawun yan sandan, SP Yesimi Opalola a yau Laraba ta bayyana cewa yan fashin da suka farmaki banki da kuma ofishin yan sanda ranar Talata da misalin kare 2 na rana sun lalata motar yaki ta hanyar harba wani makami mai fashewa.

Ta kara da cewa yan fashin sun dau tsawon lokaci suna musayar wuta da jami’an yan sanda a yayin da suka harba wasu makamai masu fashewa wanda hakan yayi sanadin lalacewar wani bangare na ofishin yan sandan bugu da kari kuma sun lalata wata motar yaki mallakin hukumar yan sanda.

A bangare guda, yayin da suka yi kokarin shiga bankin sun lalata kofar tsaro ta shiga bankin, kana kuma sun lalata na’urar cire kudi, sai di kuma kokarin su na shiga dakin ajiya na bankin bai yi nasara ba.

Jami’in yace a yayin da jami’an su ke kokarin fatattakar yan fashin, biyu daga cikin jami’an; Sufeta Ogunbiyi Ahmed da Sufeta Odeyemi Ayinla sun rasa rayukan su.

Daga karshe yan fashin sun tsere a yayin da musayar wutan ta tsananta kana kuma babu alamar gajiyawa daga bangaren yan sandan inda suka bar ababen hawa guda 2.
Hukumar yan sanda a tare da hadin gwiwar wasu jami’ai na zaga dazukan ketare don gano inda yan fashin suka tsare domin zakulo su.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Osun: ‘Yan Sanda Biyu Sun Rasa Rayukan Su Yayin Fashin Bankin WEMA”