October 1, 2021

OSUN: Mutuwar Wata Daliba A Jami’ar Awolowo Ya Haifar Da Zanga-Zangar Dalibai

Daga Muhsin Gombe


Daliban jami’ar Obafemi Awolowo na garin Ile-Ife dake jahar Osun sun yi zanga-zanga a yau Juma’a inda suka datse babbar titin Ife zuwa Ibadan da kuma titin Osogbo zuwa Ede kan mutuwar daya daga abokan karatun su mai suna Omowumi Aisat Adesina.

‘Dalibar ta kasance a zangon karshe na karatun ta a jami’ar, ta rasu da yammacin Alhamis.

 

Dalibai masu zanga-zangar sun zargi asibitin jami’ar da rashin bada kulawa da ya dace ga dalibar da ta rasa ranta kana kuma sun zargi ma’aikatan asibitin da sakaci Kari da nuna halin ko-in-kula ga marasa lafiyar da ke jiya a asibitin makarantar.

Mai magana da yawun jami’ar ta Obafemi Awolowo wato Abiodun Olarewaju ya nemi daliban da su kwantar da hankulan su, ya kuma nuna rashin dalibar a matsayin lamarin da ya sosa ran hukumar makarantar baki daya, kana kuma ya nemi daliban da su kauracewa aiyukan da zasu kawo rashin zaman lafiya da tashin hankali a cikin jami’ar.

 

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “OSUN: Mutuwar Wata Daliba A Jami’ar Awolowo Ya Haifar Da Zanga-Zangar Dalibai”