September 16, 2021

Osinbajo Zai Wakilci Najeriya A Taron ECOWAS A Ghana

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai wakilci Shugaba Muhammadu Buhari a taron da za’a gudanar a kasar Ghana na shuwagabannin kasashen Afirka ta yamma kan lamarin siyasar kasar Guinea.

Satin da ya gabata Mataimakin Shugaban kasan ya halarci taron ECOWAS din kan lamarin siyasar Mali da Guinea.
Inda aka kai ga matsayar cewa kori kasar Guinea daga gamayyar kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS.

Kana shuwagabannin ECOWAS din sun yi kiran gaggawa kan sakin shugaba Alpha Conde na kasar Guinea da sauran mukarraban sa da aka kama, sun kuma nemi wadanda suka aikata aikin hambarar da gwamnatin ta Guinea da su janye daga aniyar su da kuma dawowa kan kundin tsarin mulkin kasar.

 

Mataimakin Shugaban kasan zai samu rakiyar Ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Zubairu Dada, kana kuma ana sa ran dawowar su a daren ranar ta Alhamsi.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Osinbajo Zai Wakilci Najeriya A Taron ECOWAS A Ghana”