February 27, 2023

Oshiomhole ya lashe zaben Sanata a Edo

Tsohon Gwamnan Jihar Edo, kuma tsohon Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya lashe zaben Sanata mai waliktar Edo ta Arewa.

Oshiomhole dai ya samu kuri’a 107,110 inda ya doke Sanata mai ci, Francis Alimikhena, ma jam’iyyar PDP wanda ya sami kuri’a 55,354.

A cewar jami’in INEC mai kula da tattara sakamakon zaben, Farfesa Buniyamin Adesina Ayinde, dan takarar LP, Aslem Eragbe, ne ya zo na uku da kuri’a 15 923.

Daga Usman A. Bello, Benin da Sani Ibrahim Paki

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Oshiomhole ya lashe zaben Sanata a Edo”