October 8, 2023

​Oman: Gangamin Nuna Goyon Bayansu Ga Al’ummar Gaza

 

‘Yan kasar Omani, a wata zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Gaza, sun bukaci shelanta kai dauki domin taimaka ma gwagwarmayar Palastinawa.

Al’ummar kasar Oman sun nuna goyon baya ga al’ummar Gaza, sun kuma bukaci malaman duniyar musulmi da su ayyana wajabcin bude iyakokin kasashen musulmi ga masu aikin sa kai domin taimakon Palastinawa wanda yahudawan sahyuniya ke yi wa kisan gilla a kullum rana ta Allah tsawon shekaru.

Baya ga kasar Oman, an gudanar da irin wannan jerin gwano da gangami a kasashen musulmi da dama, daga ciki har da kasashen Yemen, Iraki, Iran, Tunisia, Aljeriya, Masar da sauransu, domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, tare da yin Allawadai da kakkausar murya kan yadda manyan kasashen duniya suka yi gum da bakunansu tsawon shekaru na kisan kiyashin da Isra’ila take yi wa al’ummar Falastinu, da kuma yadda a halin yanzu irin wadannan kasashe suke ta babatu biyo bayan mayar da martani da Falastinawa ‘yan gwagwarmaya suka yi kan yahudawan Isa’ila.

 

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Oman: Gangamin Nuna Goyon Bayansu Ga Al’ummar Gaza”