May 3, 2023

OIC : Isra’ila Ce Ke Silan Mutuwar Khader Adnan A Gidan Yari

 

Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta dora lahakin mutuwar dan fafatukar nan na Falasdinu Khader Adnan a gidan yari, kan Isra’ila.

A sanarwar da kungiyar ta yi tir da Isra’ila kan mutuwar ta Adnan tana mai cewa hakan ya faru ne saboda rashin kula da lafiyarsa.

OIC ta ce hakan na faruwa ne sakamakon matakan wuce gona da iri na Isra’ila, da cin mutuncin bil’adama da ake yi wa fursunonin Falasdinawa da kuma tauye musu muhimman hakkokin da aka ba su daga yarjejeniyoyin kasa da kasa.

Kungiyar ta OIC ta kuma tabbatar da goyon bayanta ga fursunonin Falasdinawa, tare da yin kira, a lokaci guda, ga hukumomin kasa da kasa da su gaggauta shiga tsakani domin kare masu hakkinsu, da kuma tsawatawa gwamnatin mamaya ta Isra’ila, domin kawo karshen cin zarafi da ake yi musu, da kuma gaggauta

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “OIC : Isra’ila Ce Ke Silan Mutuwar Khader Adnan A Gidan Yari”