December 12, 2022

Ofishin yakin neman zaben PDP na Gombe na ci da wuta

 

A yanzu haka ofishin yakin neman zaben Mohammed Barde, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Gombe ya na nan na cin da wuta.

Daily Trust ta rawaito cewa ana zargin wasu ƴan bangar siyasa ne su ka kona ofishin da ke kusa da masaukin shugaban kasa na gidan gwamnatin Gombe a safiyar yau Litinin.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto babu wasu cikakkun bayanai a kan harin, amma jam’iyyar PDP ta dora alhakinsa kan jam’iyyar APC mai mulki.

A wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben Atiku/Dan Barde, Junaidu Usman Abubakar ya fitar, ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce an lalata kadarori a ofishin.

“Da sanyin safiyar yau ne wasu ‘yan bangar siyasa, wadanda ake zargin na jam’iyyar APC ne su ka kai hari a ginin ofishin yakin neman zaben PDP, inda suka kona ginin tare da lalata kadarori.”

“Harin na sunkuru da aka kai wa wannan ginin, daya daga cikin da yawa a watannin baya, ya kara tabbatar da cewa gwamnatocin da ke yanzu sun tsaya tsayin daka kan tashe-tashen hankula da barna, barazana ga rashin kwanciyar hankali a jihar, wanda dole ne kowa da kowa ya tashi ya yaƙi wannan ta’ada.

“Dan takarar Gwamna a jam’iyyar PDP Alh Muhammad Jibrin Barde a lokuta daban-daban ya na Allah wadai da tashin hankali da ‘yan daba na siyasa, inda ya jaddada bukatar shigar da matasan Gombe masu hannu da shuni wajen cimma manufa mai ma’ana.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya tabbatar wa Daily Trust da faruwar lamarin, ya kuma ce an fara gudanar da bincike tare da daukar matakin cafke wadanda suka aikata laifin.

 

©Daily Nigeria

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Ofishin yakin neman zaben PDP na Gombe na ci da wuta”