January 16, 2023
Ofishin UN: Mutane Fiye Da Miliya 15 Suna Bukatar Agajin Jin Kai A Kasar Siriya

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Siriya ya jaddada bukatar aikewa da kayayyakin jin kai zuwa kasar ta Siriya
Mataimakiyar wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a kasar Siriya Najat Rushdi ta bukaci mambobin Hukumomin da suke gudanar da ayyukan jin kai a duniya da su ci gaba da bayar da goyon baya ga al’ummar kasar ta Siriya, yayin da adadin masu bukatar agaji jin kan dan Adam suke karuwa a kasar.
Madam Rushdi ta jaddada cewa: Akwai bukatar a gaggauta samar da karin kudade ga kasar ta Siriya, musamman ganin cewa, akwai mutane kimanin miliyan 15.3 da suke bukatar agajin jin kai, kuma ana sa ran adadin zai karu.