March 11, 2023

NSCDC ta kama wasu gungun mutane da jabun dalar Amurka da Naira a Plateau

 

Hukumar tsaron fararen hula ta Najeriya, NSCDC, ta cafke wasu ƴan ta’adda biyu da ake zargi da bugawa da rarraba dalar Amurka, Dala, da sabbin Naira na jabu

Daraktan hulda da jama’a na NSCDC, Olusola Odumosu ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a jiya Juma’a a Abuja.

Ya ce gungun guda biyu, inda a ka kama gungu na farko da ya kunshi mutanw hudu da dala dubu 64,800 na bogi da kuma N475,000.

Ya kuma ce an kama jabun kudi naira miliyan 1.5 daga gungu na biyu na mutane biyar.

“a cikin Naira miliyan 1.5 da aka kama, Naira dubu 784,500 na jabu ne na sabbin kudin Naira yayin da Naira dubu 49,650 na tsohuwar takardar Naira ne⁰,” inji shi.

Daraktan ya ce an kama wadanda ake zargin ne daga wurare a Filato da babban kwamandan hukumar leken asiri na musamman a tsakanin ranar 22 ga watan Fabrairu zuwa 8 ga watan Maris.

Ya ce bincike ya nuna cewa kungiyoyin sun shafe shekaru suna gudanar da ayyukansu a yankin Plateau, Nasarawa, Bauchi da Gombe.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “NSCDC ta kama wasu gungun mutane da jabun dalar Amurka da Naira a Plateau”