NNPC ta kara farashin man fetur a fadin Najeriya

Kamfanin man fetur na Najeriya ta kara farashin litar mai a duk fadin jihohin kasar. Wannan na zuwa ne bayan bayanin da sabon Shugaban Kasar Bola Ahmed Tinubu yayi a yayi rantsuwa inda ya bayyana cewa babu cigaba da tallafin man fetur a Najeriya. Wannan dai ya samo asali ne tun daga gwamnatin da ta shude inda ta yi ta zaftare tallafin har kuma daga karshe ta nuna bazata iya cigaba da jurar biyan tallafin ba.
NNPC dai ta kara farashin litar mai din ne bisa la’akari da jihohi. Karin farin kamar haka:
Farashin lita guda a jiihar Pilato ya tashi daga N189 zuwa N537.
Kwara N189 zuwa N515
Kogi N189 zuwa N537
Benuwai N189 zuwa N537
Naija N189 zuwa N537
Adamawa N199 zuwa N550
Taraba N199 zuwa N550
Bauchi N199 zuwa N550
Gombe N199 zuwa N550
Borno N199 zuwa N557
Yobe N199 zuwa N557
Kano N194 zuwa N540
Kaduna N194 zuwa N540
Katsina N194 zuwa 540
Kebbi N194 zuwa N545
Zamfara N194 zuwa N540
Sokoto N194 zuwa N540
Jigawa N194 zuwa N540
Abia N189 zuwa N515
Imo N189 zuwa N515