October 2, 2023

NLC ta dakatar da yajin aiki bisa wasu Sharuda.

Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC sun amince da janye yajin aikin da aka shirya gudanarwa ranar 3 ga watan Oktoba, 2023, a matsayin martani ga kawar da tallafin man fetur.

Majalisar zartaswar NLC ta kasa ta bayar da umarnin cewa dukkan mambobinta da su umarci mambobinsu da su koma bakin aiki a gobe 3 ga Oktoba, 2023 saboda an dakatar da yajin aikin da aka shirya yi.

Sai dai bayan taron gaggawar da aka kira yau 2 ga watan Oktoba 2023 tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kwadago, NLC da TUC sun amince tare da dakatar da yajin aikin domin samun damar aiwatar da bukatun kungiyar ta NLC.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “NLC ta dakatar da yajin aiki bisa wasu Sharuda.”