May 20, 2023

(NiMET) tayi hasashen cewa akwai yiwuwar fuskantar ambaliya mai girma a daminan bana.

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar da sanarwar cewa ana hasashen bana ma za a yi ruwan sama sosai, inda ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar fuskantar ambaliya mai girma.

Idan ba a manta ba, a bara an fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani, wadda ta jawo asarar rayuka da miliyoyin Naira.

A shekarar da ta gabata an samu matsalar ambaliyar ruwa a jihohidaban-daban a Naieriya, a Jihar Taraba, fiye da garuruwa 100 ne suke bakin manyan kogunan jihar wadanda suka fuskanci matsalar ambaliya a bara.

Wadannan garuruwan suna cikin kananan hukumomi takwas daga cikin 16 da ke jihar. Kananan hukumomin sun hada da Lau da Karim Lamido da Gassol da Ibbi. Sai ArdoKola da Wukari da Donga da Bali .

Dubban al’ummar wadannan yankuna suna gudanar da ayyukan noma a gaban koguna da ake samun matsalar ambaliya a lokuta da dama.

Kogunan sun hada da Kogin Binuwai da na Taraba da Kogin Lamurde da kuma Kogin Donga.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “(NiMET) tayi hasashen cewa akwai yiwuwar fuskantar ambaliya mai girma a daminan bana.”