September 13, 2023
Nijar Ta Yanke Huldar Soji Da Ke Tsakaninta Da Benin

Sabbin mahukunta a Nijar sun yanke huldar soji da ke tsakaninsu da makwabciyarsu Benin, suna masu zarginta da bari a yi amfani da kasar domin jibge sojoji da kayan yakin da ECOWAS za ta yi aiki da su don yiwuwar kai musu hari.
A wata sanarwa da sojojin suka karanta a gidan talabiji na kasar ranar Talata, sun ce Benin ta “bayar da umarni a yi amfani da sojoji da sojojin haya da kayan yaki” domin ECOWAS ta kai musu hari.
Don haka, sojojin na Nijar suka “yanke shawarar soke dangantaka da kawancen soji [da Benin],” in ji sanarwar.
Kawo yanzu Benin ba ta mayar da martani ba.
A karshen makon jiya ne Nijar ta yi zargin cewa Faransa tana tura sojojinta zuwa kasashen Yammacin Afirka da dama da zummar yin amfani da “kafin soji” a kansu.
©voh