May 17, 2023

Nigeriya: Mutane 4 Ne Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci 2 Daga Cikinsu Ma’aikata Karamin Ofishin Jakadancin Amurka Ne.

 

Wasu yan bindiga sun yi barin wuta kan tawagar motoci na karamin ofishin jakadancin Amurka dake Jihar Anambara na kudu maso gabacin tarayyar Najeriya a jiya Talata, inda suka kashe mutane 4, suka raunata wasu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ikenga Tochukwu mataimakin superintendent na yan sanda a Jihar yana fadawa tashar talabijin ta CNN kan cewa biyu daga cikin wadanda aka kashe ma’aikatana ne a karamin ofishin jakadan Amurka dake jihar, amma ba sa yan kasance na Amurka.

Labarin ya kara da cewa yan bindigan wadanda har yanzun ba’a fayyace ko su waye ne ba, da kuma abinda sune bukata da wannan kissan ba, sun kona gawakin mutanen da suka kashe sun kuma tsere daga wurin bayan haka.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Nigeriya: Mutane 4 Ne Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci 2 Daga Cikinsu Ma’aikata Karamin Ofishin Jakadancin Amurka Ne.”