May 18, 2023

Nigeria: A Kalla Mutane 30 Ne Su Ka Rasa Rayukansu A Fadan Makiyaya Da Manoma

Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Nigeria sun ce, mutanen 30 sun kwanta dama ne sanadiyyar wani fada da ya barke a tsakanin manoma da makiyaya a jihar Filato dake tsakiyar kasar.

Kwamishinan watsa labaru na jihar ta Filato Dan Manjang ya fadawa kamfanin dillancin labaru AFP cewa; Fiye da mutane 30 ne su ka rasa rayukansu sanadiyyar rikicin wanda ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata.

Kwamishinan na watsa labaru na jihar ta Filato ya kuma ce; Mafi yawancin mafi yawancin makiyayan dai musulmi ne, yayin da mafi yawancin manoma kuma kiristoci ne.

Su kuwa jami’an ‘yan sanda sun ce, an yi rikicin ne a garin Bwoi da yake yankin Mangu,inda su ka sami kira da misalin karfe;11;56 na cewa ana yin harbe-harbe.

Kakakin ‘yan sanda Alfre Alabo ya kuma ce tuni an aike da jami’an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru,inda su ka yi fafutuka da masu dauke da makamai.

Yankunan Arewa maso gabashin Nigeri ada kuma tsakiyarta suna daga cikin wuraren da akan sami tashe-tashen hankula irin wadannan a tsakanin manoma da makiyaya.

. A watan Aprilu da ya shude, mutane 50 ne aka kashe a wani hari da aka kai a wani kauye dake jihar Benue mai makwabtaka da Filato.

Shugaban karamar hukumar ta Mangu ya sanar da kafa dokar ta baci na tsawon sa’o’i 24, domin tabbatar da cewa rikicin bai watsu da nisa ba

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Nigeria: A Kalla Mutane 30 Ne Su Ka Rasa Rayukansu A Fadan Makiyaya Da Manoma”