October 17, 2021

Nasarawa: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu daliban jami’ar Lafiya

Daga Balarabe Idriss


‘Yan bindiga sun kai farmaki unguwar Mararaba Akunza wanda yake yanki ne na jami’ar tarayya ta Lafiya da ke karamar hukumar Lafiya ta jihar Nasarawa inda suka yi awun gaba da wasu mutane 4 da suka kasance dalibai a jami’ar.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 7 zuwa 8 na daren jiya Asabat a yayin da ake tsaka da ruwan sama.

Wani mutum daga shaidun gani da ido ya shaida cewa ‘yan bindigan sun zo ne cikin zuga da bindigogi kira AK 47 kana kuma suka fara harbi a sama na tsahon lokaci kafin su dauki daliban su yi awun gaba da su.

Wata majiya ta shaida cewa ‘yan bindigan sun kira wasu daga dangin daliban da suka yi garkuwa da su din da misalin karfe 11:30 inda suka nemi kudin fansa da ya kai kimanin naira miliyan 25.

Har wala yau rahoton ya sake jaddada cewa daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su din mai suna Zafir Yahaya, d’a ne ga Malam Yahaya Adams wanda ya kasance daya daga manyan yan siyasa a jahar.

Sai dai kuma duk da hujjojin da suka bayyana, jami’in hulda da jama’a na jami’ar ta Lafiya Malam Abubakar Ibrahim ya musanta cewa wadanda aka yi garkuwa da su din daliban jami’ar ne, inda ya bayyana cewa babu wani dalibin su da aka yi garkuwa da shi, hasali ma lamarin ya faru ne a wajen jami’ar ba cikin ta ba.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan jahar Nasarawa, ASP Nansel Rahman ya bayyana cewa tuni bayan faruwar lamarin jami’an su sun bazama daji don bincike da kuma bin sawu. Sani dai kuma har wala yau jami’in yace zuwa yanzu basu samu wani korafi daga hukumar jami’ar ba.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Nasarawa: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu daliban jami’ar Lafiya”