November 28, 2021

Nan Ba Da Daɗewa Ba Rundunar Sojin Ruwan Nijeria Za Ta Ƙaddamar Da Ƙungiyar Wasan Ƙwallon Dawaki

Daga Baba Abdulƙadir


Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta fara aikin ganowa tare da tantance jami’anta da suke bugawa ko sha’awar wasan ƙwallon dawaki na polo domin kafa ƙungiyarta.

Shugaban rundunar sojin ruwan ta Nijeriya, Vice Admiral Awwal Gambo, ne ya bayyana hakan yayin bikin rufe gasar wasan ƙwallon dawaki karo na tara da aka gabatar a filin wasan ƙwallon dawaki na garin Keffi, ta jihar Nassarawa, inda ya jaddada cewa hakan zai bayar da gudunmawa gurin ci gaban wasan a Nijeriya.

Ya bayyana cewa rundunar sojin ruwan Nijeriya ta fara wasan ƙwallon dawaki a hukumance ta hanyar wata gasar ƙwallon dawaki da ƙungiyar Gwards Brigade Polo Club ta shirya a matsayin ɗaya daga cikin shirye-shiryen taron shekara-shekara na shugaban sojin ruwan Nijeria, shekarar 2021.

A cikin wani jawabi da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin ruwan, Commondore Suleiman Dahun, ya fitar ya bayyana cewa Admiral Gambo ya gano cewa kasancewarsa wasa na tawaga, wasan yana haskaka amfanin gina sadarwa mai ƙwari, samar da dabarar shugabanci da kuma ƙwarewar gabatar da aiki a tare tsakanin ƴan wasa.

Ya ƙara da faɗin cewa waɗannan abubuwa ne da za su yi amfani gurin inganta taimakekeniya da aiki a tare tsakanin jami’ai a gurin aiwatar da aikin samar da tsaro ga ƙasa.

Shugaban sojin ruwan ya yaba wa waɗanda suka haɗa gasar sakamakon haɗa abun da yake bayar da goyon baya ga ci gaban ilimi a Nijeriya. Admiral Gambo ya bayyana cewa ilimi shi ne babban abun da ya kamata a bar wa ƴan baya. Hakan ya sanya rundunar sojin ruwan Nijeriya take jajircewa gurin inganta ilimin ƴaƴan jami’anta da kuma yara da matasan al’ummar da suke zaune a ciki ta hanyar kafa makarantu a duk faɗin ƙasar.

Ya ƙara da faɗin cewa rundunar sojin Nijeriya tana cikin aikin yunƙurin samar da makarantu masu aminci da ake yi domin samar da yanayi na karatu mai aminci da tsaro ga yara da matasa a faɗin ƙasa bakiɗaya.

Shugaban rundunar sojin ruwan ya kuma tabbatar da cewa haƙiƙa gasar aba ce me kyau sannan kuma hanya ce ta gina rayuwar yara da matasa a nan gaba. Ya kuma bayyana farin cikin rundunar sojin ruwan Nijeriya na kasancewa a cikin wannan abun na a yaba, inda ya ƙara cewa yunƙurin ya bayar da gudunmuwa mai kyau ga yunƙurin gwamnatin tarayya na samar da ilimi mai inganci ga yara da matasan Nijeriya.

Shugaban ya kuma yaba wa uban ƙungiyar wasan ƙwallon dawakin Keffi Polo Ranch, Ahmed Aliyu, da mambobin kwamitin shirya gasar sakamakon gudanar da gasar wadda ta shafe tsawon sati ɗaya ana gabatarwa.

SHARE:
Labarin Wasanni 0 Replies to “Nan Ba Da Daɗewa Ba Rundunar Sojin Ruwan Nijeria Za Ta Ƙaddamar Da Ƙungiyar Wasan Ƙwallon Dawaki”