August 18, 2021

Najeriya Za Ta Jinginar Da Filayen Jiragen Sama

Daga Baba Abdulƙadir

Hukumar kula da harkokin sufirin jiragen sama ta Najeriya, ta bayyana aniyar ta ta baiwa masu sha’awar jinginar manyan filayen jirgin saman zirga-zirgar ƙasashen waje guda 4.

Hakan na cikin wata sanarwa da babban sakataren hukumar Injiniya Hassan Musa, ya sanya wa hannu a yau Litinin.

Sanarwar hukumar ta ce, filayen da za a bada jinginar sune: na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da filin jirgi na Murtala Muhammed da ke jihar Legas sai na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano da kuma filin jirgin sama na birnin Fatakwal ( Port Harcourt)

                      Filin jirgi na Murtala Muhammad da ke jihar Legas

 

                        Filin jirgi na Nnamdi Azikwe da ke birnin Abuja

 

                   Filin jirgin Aminu Kano da ke jihar Kano
                                    Filin jirgin Fatakwal

Hakazalika sanarwar ta ce, bayar da jinginar filayen jirgin saman ya yi dai-dai da tsarin hukumar kula da jinginar kadarorin gwamnati ta ICRC da ta bada damar yin hakan ta hanyar neman masu sanya hannun jari a kadarorin gwamnatin tarayya.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Najeriya Za Ta Jinginar Da Filayen Jiragen Sama”