September 2, 2023

Najeriya ta yi kira ga MDD da ta kara tallafawa kasar yaki da ta’addanci

Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, ya gana da mataimakin sakataren MDD mai kula da harkokin yaki da ta’addanci Vladimir Voronkov, a birnin Abuja fadar mulkin kasar, inda ya yi kira ga MDD da ta kara tallafawa kasar wajen yaki da ta’addanci.

Rahotannin da fadar shugaban kasar ta fitar a jiya Juma’a, sun ce Bola Tinubu ya soki akidun ta’addanci, a matsayin abubuwan da suka illata ci gaban kasar, da zaman lafiyar al’umma, yana mai fatan MDD za ta kara goyawa gwamnatin sa baya, kasancewar ba za a iya tabbatar da bunkasuwa da wadata ba, karkashin kalubalen ta’addanci.

A nasa bangare, Vladimir Voronkov, ya ce Najeriya ta taka rawar gani a fannin yaki da ta’addanci a duniya, kuma majalisar na shirin gudanar da taron koli na yaki da ta’addanci a watan Afrilun shekarar badi, inda za a mai da hankali kan wannan batu a Afrika.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Najeriya ta yi kira ga MDD da ta kara tallafawa kasar yaki da ta’addanci”