May 6, 2023

​Najeriya Ta Sake Kwaso Wasu ‘Yan Kasarta 130 Daga Sudan

 

Karin ’yan Najeriya 130 daga cikin wadanda suka makale bayan barkewar yaki a kasar Sudan sun sauka a Abuja a yammacin ranar Juma’a.

Jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa, mutanen sun dawo gida ne a daidai lokacin da kasar Masar ta tisa keyar wasa ’yan Najeriya kimanin 500 zuwa Sudan, bayan sun tsallaka zuwa cikin kasarta neman tsira.

Masar ta dauki matakin ne bayan da wasu daga cikin ’yan Najeriyar da aka kwashe daga Khartoum, babban kasar Sudan, zuwa kasar Masar suka lakada wa jami’an tsaronta duka.

’Yan Najeriyar da ake zargi sun yi hakan, lamarin faru ne bayan takaddamar da ta barke tsakaninsu da jami’an tsaron Masar filin jirgi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Najeriya Ta Sake Kwaso Wasu ‘Yan Kasarta 130 Daga Sudan”