September 26, 2023

Najeriya ta fara shirye-shiryen bikin cika shekaru 63 da samun ’yanci

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da jadawalin tsare-tsaren bukukuwan bikin cikar kasar shekaru 63 da samun ’yanci wanda zai kama ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba.

Sakataren gwamnatin tarayyar Mr George Akume ne ya sanar da hakan jiya Litinin yayin taron manema labarai a birnin Abuja, sai dai ya ce a bana za a yi bikin ne ba tare da shagulgula ba kamar yadda aka saba, sannan kuma ba za a gayyaci shugabanni daga wasu kasashe ba.

Sanata George Akume ya ce, shugaban kasa ne ya bayar da izinin gudanar da bikin ba tare da yin hidindimu ba sakamakon yanayin matsin tattalin arziki, kuma an yi wa bikin na bana lakabi da “Sabunta kyakkyawan fata na hadin kai da wadatar arziki”.

Na farko dai daga cikin abubuwan da za a gudanar domin sheda wannan rana ya hada da taron manema labarai na duniya wanda shi ne muka gudanar a wannan rana ta Litinin 25 ga wata.

“Za a gabatar da kasidu da muhawara kan shekaru 63 na kasancewar Najeriya kasa mai ’yanci a ranar Alhamis 28 ga wata a babban dakin taro dake fadar shugaban kasa. Sai na uku kuma taron lacca a babban masallaci na kasa dake Abuja da misalin karfe 10 na safe yayin da za a gudanar da sallar Juma’a da karfe 1 na rana, sai ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba, shugaba Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasa da misalin karfe 7 na safe, yayin da kuma da misalin karfe 10 na safiyar Lahadin za a gudanar da addu’o’i a cibiyar mabiya addinin Krista ta kasa dake Abuja. A ranar Litinin 2 ga watan Oktoba, za a gudanar da fareti na musamman a fadar shugaban kasa da misalin karfe 9 na safe.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Najeriya ta fara shirye-shiryen bikin cika shekaru 63 da samun ’yanci”