January 30, 2024

​Najeriya: Sojoji Sun Halaka ’Yan Bindiga Da Dama A Kaduna

Wasu ’yan bindiga kimanin 30 sun sheka lahira a wani luguden wuta da jiragen sojin Najeriya suka yi musu a yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Jiragen sun jefa wa ’yan bindigar bom ne a yankin Kwiga-Kampanin Doka da ke Birnin Gwari bayan samun bayanai kan shirinsu na kai hari.

Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Edward Gabkwet ya ce, “Jiragen yaki sun gano su ne a wani wuri da suka taru, inda aka jefa musu bom, aka hallaka mafi yawansu.”

Edward Gabkwet ya bayyana cewa an gano dandazon ’yan ta’addan ne a kan baburansu a lokacin da suke kan hanyarsu ta kai hari, aka jefa musu bom aka kashe.

Jami’in ya ce ’yan bindigan da jiragen suka kashe din ne suka addabi Karamar Hukumar Birnin Gwari, inda suka kai wa sojoji harin kwanton bauna a yankin Kwanar Mutuwa a ranar Asabar.

A cwearsa, ’yan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne a hannun dakarun rundunar soji ta Operation Whirl Punch.

©VOH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Najeriya: Sojoji Sun Halaka ’Yan Bindiga Da Dama A Kaduna”