April 30, 2023

​Najeriya: Shugaba Buhari Ya Bada Umurnin Dakatar Da Shirin Kidayar Mutanen Kasar Na Wannan Shekara

Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya bada umurnin dakatar da shirin kidayar mutane da gidaje a kasar wanda aka shirya gudanar da shi a ranaku 3-7 ga watan Mayu mai kamawa.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ministan watsa labarai Lai Muhammad yana fadar haka a wata sanarwan da ya fiyar a rubuce bayan taron wasu daga cikin majalisar ministocin kasar tare da shugaban kasa a fadarsa a ranar Jumma’a.

Labarin ya kara da cewa lalle ana bukatar kidaya a kasar bayan shekaru 17 daga na karshe da aka gudanar, kuma kidayar ta zama dole don da shi ne gwamnatoci masu zuwa su tafi suke iya tsara al-amuran ci gaban kasa.

Banda haka shugaban ya bukaci hukumar kidaya ta kasa ta ci gaba da shirin gudanar da kidayar zuwa lokacinda gwamnati mai shigowa zata sanya sabin kawanaki na kidayar nan gaba.

Minmistocin da suka sami halattan taron na ranar Jumma’a dai suna hada da na Sharia, Kudi, Wasta labarai, sakataren gwamnati da kuma karamin ministan kasasfin kudi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Najeriya: Shugaba Buhari Ya Bada Umurnin Dakatar Da Shirin Kidayar Mutanen Kasar Na Wannan Shekara”