Najeriya: Sa’o’ii 96 Suka Ragewa Gwamnatin Buhari, Amma Kamfanin Jiragen “Nageria Air” Bai Fara Aiki Ba

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta kara da cewa ministan ya kara jaddada wannan batun a ranar litinin da ta gabata bayan taron majalisar ministocin kasar a fadar Aso Rock wanda mataimakin shugaban kasa ya jagoranta. Ministan ya kara jaddawa cewa an kammala dukkan shirye-shirye na ganin kamfanin ya fara aikin kafin karshen wannan gwamnatin.
Labarin ya kara da cewa a ranar 19 ga watan Fabarairun da ya gabata ne shugaba Buhari ya gana da shugaban kamfanin jiragen sama na “Ethiopian Air” Girma Wake inda suka tattauna batun kaddamar da kamfanin na Najeria Air, sai dai kafin haka Wake ya bayyanawa bangaren Najeria a wani taron da aka gudanar a birnin Adis Ababa kan cewa yana bukatar a warware matsalar sharia ko kuma dokoki wadanda suka hada ci gaba a kaddar da kamfanin zirga zirgan jiragen sama na ‘Nigeria Air’.
Tun shekara ta 2019 ne ministan zirga-zirgan jiragen sama na kasar ya bayyana shirin samar da kamfanin.