April 12, 2023

​Najeriya: Majalisa Ta Gayyaci Ministar Kudi, Sakataren Gwamnati Kan Bacewar Dala Biliyan 2.4

‘Yan Majalisar wakilan najeriya sun gayyaci Ministar Kudi da Sakataren Gwamnati, NNPC da sauran su kan batun dala biliyan 2.4 da aka sace

Tashar Channels ta bayar da rahoton cewa, Kwamitin ya nuna damuwa game da bambance-bambancen alkaluman sayar da danyen mai daga shekarar 2011 zuwa 2014.

Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai kan satar mai yana gayyatar wasu manyan jami’an gwamnatin tarayya kan binciken da ta yi kan asarar sama da dala biliyan 2.4 na kudaden shiga daga sayar da ganga miliyan 48 na fitar da danyen mai ba bisa ka’ida ba a shekarar 2015.

Wasu daga cikin jami’an da aka gayyata a ranar Talata domin amsa tambayoyi sun hada da ministar kudi, Zainab Ahmed; da Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya ruwaito.

Haka kuma an gayyaci mukaddashin Akanta Janar na Tarayya, Sylva Okolieaboh; da Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), da dai sauransu.

Kwamitin ya kuma nuna damuwa game da bambamcin alkaluman da ake samu daga sayar da danyen mai daga shekarar 2011 zuwa 2014 kuma yana zargin ministan kudi da amincewa da biyan wasu masu fallasa kudaden da aka saba da manufar yin fallasa.

Kwamitin wucin gadi na majalisar ya binciki zargin sayar da gangar danyen man fetir din Najeriya ganga miliyan 48 ba bisa ka’ida ba a kasar Sin a shekarar 2015, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 2.4.

Kwamitin, a watan Fabrairu, ya zargi Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami da kuma Interpol, kan abin da ya bayyana a matsayin katsalandan a binciken kwamitin.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Najeriya: Majalisa Ta Gayyaci Ministar Kudi, Sakataren Gwamnati Kan Bacewar Dala Biliyan 2.4”