August 9, 2021

Najeriya: Kwamandan Кera Bama-Bamai Na Boko Haram Da Wasu Mataimakansa Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Daga Jaridar “Hausa Radio Iran”

Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar babban kwamanda mai kula da ɓangaren ƙera nakiyoyi da bama-bamai na ƙungiyar Boko Haram, Amir Abu Darda tare da wasu ƙwararrun mataimakansa sun miƙa kansu tare da makamai da wasu kayayyakin aikinsu ga sojojin Najeriya a yankin arewa masu gabashin ƙasar.

Jaridar Vanguard ta Nijeriya ɗin ce ta buga wannan rahoton inda ta bayyana cewa wata majiya ce ta bayyana mata hakan.

Har ila yau jaridar ta ce cikin ‘yan kwanakin nan kimanin ‘yan ta’addan Boko Haram ɗin 300 ne suka mika kan su ga sojojin na Nijeriya da suke gudanar da ayyukansu a yankunan arewa maso gabashin Nijeriyan.

Haka nan jaridar ta ce bisa ga bincike mafi yawa daga cikin ‘yan ta’addan da suka mika kan na su sun fito ne daga dajin nan na Sambisa da kuma yankin Tafkin Chadi sakamakon ci gaba da luguden wuta da sojojin Nijeriyan suke musu a waɗannan yankunan ta ƙasa da sama.

Kaimin hare-haren da sojojin Nijeriyan suka ƙaddamar a baya-bayan nan yana zuwa ne bayan wata ziyara da sabon babban hafsan hafsoshin sojin ƙasa na Nijeriyan Laftanar Janar Farouk Yahaya ya kai wa dakarun Nijeriyan a yankunan arewa maso gabashin Nijeriya inda ya tabbatat musu da dukkanin goyon bayan da suke buƙata wajen faɗa da suke yi da ‘yan ta’addan da kuma ‘yan fashin daji masu garkuwa da mutane.

Babban hafsan ya buƙaci sojojin da su ba da dukkanin ƙarfinsu wajen ganin sun kawo ƙarshen ‘yan ta’addan, gwamnati kuma za ta ci gaba da goya musu baya.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Najeriya: Kwamandan Кera Bama-Bamai Na Boko Haram Da Wasu Mataimakansa Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji”